🇨🇮Ma'asumah Nigerian News Update
____________________
_Da sunan Allah mai daukaka adalai tsira da aminci su tabbata ga annabi da ahali tsarkaka.
_Akace mana kuma, duk wanda ya shiga aljanna, to a kalla kyau da yake dashi shine kyan annabi Yusuf(AS).
_Annabi Yusuf dinnan da matar Waziri ta tattara mata da suka zargeta cewa ta nemi yaron gidanta.
_Tace aiku ba a jarance ku da abin da aka jarabce ni dashi bane. Sai ta tattaracsuta shirya su a shimfidu, suna duban juna ta basu matasai suka dan kishingida. Tabasu dan abin tabawa da wukake na yankawa.
_Sai tacewa Yusuf yafito. Da suka ganshi, basu san lokacin da suka dinga yayyanka hannuwansu ba, suna kallo. Sai da yahuce sannan sukaga hannuwansu da jini. Suna kallon kyu ne.
_To wannan kyaune da allah yayi wa Annabi Yusuf a nan duniya. Akace duk wanda ya shiga Aljanna, in ma akwai munmuna Aljanna, to yana da kyan Annabi Yusuf (AS) ne, mafi karancin kyau danba munmuna a Aljanna.
_Wato mafi karancin kyau a Aljanna shine kyawun Annabi Yusuf (AS). Kaga inda munmuna shine wannan kenan. Kuma kowane mutum kyansa ya wuce nan. Wannan shine mafi karanci, wanda kuma suka yi gaba duk sun wuce wannan. To saidai kyawun mutum daidai kyawun dabi'unsa. Sabo da matsayinka a Aljanna da halittar da za ayimaka.
INSHA ALLAH ZAMU TSAYA ANAN AMMA ZAMUCI GABA
Masha Allah 🙏
Daga Wakilinmu Na Kano
MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com
Tags:
Taskar ilimi