Hikima Kayan Mumini Ce A Koda Yaushe!!! Babi Na Biyu (2)

🇨🇮Ma'asumah Nigerian News Update

_____________________

_Na'am a nan Allah yayi mana halitta yadda yaso, shi yabamu siffofinmu, yadda duk muka ga kanmu hakanan Allah yayimu, haka Allah ya gadaman yi. To amma gobe kiyama Allah zai canza mana halitta, zai bamu wata suffa, zatayi kama da tamu dinnan, amma kuma zakasamu tasirin ayyikanmu bayyane acikin siffofinmu. Masu kyawawan ayyuka zasu zama kyawawa, masu munanan ayyuka zasu zama munana.

_A nan nakan ga masu zane sukan yi wani abu, kunsan wani abu da ake cewa 'Catoon', a jarida akan zana abu kamar wata halitta ta daban. Wato abin da mai zancen yake nufi, yana nufin ya nuna mummunar dabi'ar mutumin da ya zana din ne.Za kaga wadansu mutane sunayin wannan irin 'Catton' din. Akan nuna talabijin, wani akan sa a jarida. Da ma galiba a jaridu akafi zanawa. Sai kaga sunyi mutum sun kamanta shi da wani abu. Alal misali na taba ganin an kamanta wasu mutane guda biyu, daya aka yi masa katantawar Dodon Kodi a baya. Sai aka nuna shi kunkurun shine shugaban kasa, Dodon Kodin kuma shine mataimakinsa.

_Sai ana cewa yana ce masa "ka yiwo sauri tafiyar fa na da nisa." Wato suna nufin cewa su wadannan mutane suna tafiya dikin-dikin, wato sunki suyi tafiya. Amma in ka gani  za ka gane su sosai. Da ganin hular shi kunkurun ka san wanene. Daga ganin kuma sifar shi(mataimakin)zaka gane shi. Wato dai abin da nake kokarin ince shine, kaga a nan suna zana mutum, amma daka gani zaka gane cewa wane ake nufi,duk da sun yi masa mummunar kama. Ko da sun kamanta shi da Alade ne ko Kare, in dai wane suke nufi, daka gani zaka gane cewa wannan wanene. To wannan shigen irin wannan kenan. Kaga a nan ma dan Adam yana yi, to ballantana  Allah Mahallici.

_Allah Ta'ala yana iya yin Alade mummuna ko jaba mummuna, amma mutanen da suka san mutumin a duniya in suka hango shi za suce wancan wane ne, in sun ganshi a wuta. Za suce wane gashi can amma anyi masa halittar Gursunu. Da za a yi mutum a Aljanna shi kuma ayi shi mai kyau, ayi shi kyakkyawan gaske. Ko yaya ya kasance a nan duniya (Saboda muni), to in kagan shi zakace wane ne, amma yanzu ya zama kyakkyawa. Wato Allah Ta'ala zai iya bashi siffarsa ta duniya da kyakkyawar kama.

INSHA ALLAH ZAMU TSAYA ANAN ZAMUCI GABA

Masha Allah 🙏

Daga Wakilinmu Na Kano

MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com


KUKASANCE DA SHAFIN MA'ASUMAH AKO DA YAUSHE DOMIN ILIMAN TUWA DAKUMA SANIN YADDA DUNIYA KECIKI.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post