Hikima Kayan Mumini Ce A Koda yaushe!! Babi Na Daya (1)


 Babi Na Daya(1)

🇨🇮Ma'asumah Nigerian News Update

_____________________

Da sunan Allah, mai murkushe Azzalumai tsira Da aminci su tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad da Iyalan sa tsarkaka.

_Shaksiyar Mutum ace shi wani ne, to lallai alal hakika shine shi. Domin kuwa idan kaga mutum, farkon ganinka dashi, yadda jikinsa ya bayyana, kila da shi zaka auna kace shi kazane. Kamar alal misali: kace shi wannan mutumin fari ne ko baki ne, dogo ne ko gajere ne, tsoho ne ko yaro ne, ko abin da yayi kama da haka nan. Amma in ka zauna dashi kuka saba, kuka dade tare to, in kagan shi, yanzu wani abu kake kallo, dabi'un sa kake kallo tunda yanzu kasan shi.

_Mu kaddara wannan mutumin yana da kyawun halitta da hancin sa mai kyau, da gashinsa mai kyau, kuma mutum ne mai tsafta, rigunan sa fes-fes. Amma da aka zauna dashi sai akaga mai mugum hali ne. Bari muce alal misali: da aka zauna dashi sai aka gane cewa shi barawone, yana dauke-dauke. To ranar da yazo fes-fes da kyakkyawan tufar nan tasa yana gabatowa, a ranka wa kake ganin yana zuwa ?  Barawo kake gani ko! Yanzu kaga an fara kaffa-kaffa. Kaga a nan kyawun sa ya zama abin da bahaushe ke cewa kyawun dan maciji. Saboda yanzu ba kuma kyawun kake ganiba, mummunar dabi'ar sa kake gani. Kaga anan ya nuna maka dabi'a (Itace mutum).

_Na'am muna iya cewa sifa zahiran Allah yayi wa mutum dama bashi yayi wa kansa ba, koda shi kyakkyawa ne na halitta, wannan inma da wanda za'a yabawa a kan kyawun sa, sai a yabawa Allah wanda yayi  masa halitta. To, amma wannan mummunar dabi'ar shi yayiwa kansa, ba Allah yayi masa ba. Kaga wannan shine a hakikani ba halittar sa ba. To kuma kaga gobe kiyama ladan me za'a bashi, ko kuma laifin me za'a kamashi dashi, ko da me za'a yi masa hisabi?.Da dabi'ar sa ko da halittar sa?Dama ita halitta Allah ne yayi masa ita yadda yaso. Kaga ashe dabi'ar mutum shine shi.

_Hadiya ga ruhin Maulana Sayyid zakzaky(H)

ZAMUTSAYA ANANZAMUCI GABA INSHA ALLAH

     Masha Allah🙏
Daga Wakilinmu na Kano

@MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com

KUKASANCE DA SHAFIN MA'ASUMAH DOMIN ILIMAN TUWA DA SANIN YADDA DUNIYA KE GUDANA

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post