2-Abu na Biyu dan gane da rufe jiki Shine A lokacin Sallah
-Mutum namiji dole ya rufe al'aurarsa, koda babu wanda zai ganshi, kana iya ihtiyaɗi bayan ka rufe daga cibiya zuwa guiwa.
KARANTA WANNAN:- Hijabin Tufafi (1)
-Mace wajibi ne ta rufe dukkan jikinta ya haɗa da gashinta da kunnenta. Saidai: fiska (goshi zuwa haɓa, da kuma babbar yatsa zuwa tsakanin yatsar tsakiya), hannu (daga guiwa zuwa ƙasa) ita kuma ƙafa zuwa idon sawu. wajibi ne ka rufe waɗannan rabe-raben gaba izuwa 'Min Babil muqaddamah'.
-Ga mace ba wajine gareta ta rufe ado ko kwaliyar fiskarta ba a yayin sallah.
-Ida da yiwuwar wani ko da tunanin wani zai iya ganin fiskarta, hannunta da ƙafarta, da kallo irin na sha'awa yayin sallah, to, wajibi ne ta rufe waɗannan sashin, ba sabida Sallah ba, a'ah saidai don waɗancen dokokin da suka gabata.
-Insha Allah ku kasance dani domin samun ci gaban wannan rubutu.....
____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ