A jiya Asabar 18/01/2020 yan uwa musulmi almajiran sayyed Zakzaky (H) na da'irar Guidan Roumji dake jamhuriyar Niger bagaren Harisiwa suka gabatar da gaggarimin aikin gayya na sharar wata hanya da ta ceke da rairayi /yashi wanda ke takurawa masu ababen hawa harma da masu takawa a kafa
Aikin ya gudana ne bisa babbar hanyar nan da ta fita daga cikin gari zuwa Bakatsomuba har ta wuce zuwa wasu kauyukka
ga kadan daga hotunan da muka dauko maku a wurin aikin gayyar Da fatan Allah ya kai Ladar ga Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H)
#Freezakzaky