@Ma'asumah Nigerian News Update, tareda Bin Haroun Sigau.
Mutane suna yawan ƙorafi kan cewa wayar su ta Smartphone ɗin su tana sha musu caji, alhali suke maishe ta mai shan cajin.
Zanyi bayanin kaɗan daga hanyoyin da zaka bi don magance wannan matsala ɗin.
Abu Na farko: Yawan saka caji; Dole ne mu kiyaye da wannan matsala domin tana da matsala sosai ga lafiyar batirin wayar mu. Dole duk wani mai son kiyaye lafiyar batirin sa ta hanyar barin batiri har sai cajin sa yayi ƙasa da %50 kana ya saka wayar sa a caji. Masu saka waya a %70 ko %90 zuwa %100 lallai wannan yana daga cikin abinda ke saka wa batirin ku yake rage riƙe caji.
Abu na Biyu: Saka caji A Computer ta USB ko kuma Power Bank, wannnan shima abune dake saurin rage ƙarfin batiri yana da kyau a kiyaye wannan!
Abu Na Uku: Shin Sanyaya waya, da yawan mutane zaka gan wani yakan bar wayarsa 24h Data a kunne. Waya tana bukatar hutu ita kanta, duk lokacin da wayar ka tayi zafi domin kare lafiyar batirin ka dole ka kashe Data, Wifi Ko Bluetooth da sauran su domin ta sanaya kafin zuwa wani miƙidarin lokaci Ko ta hanyar yin Amfani da Application mai Suna 'Cooler' zaku
iya samun Application ɗin a Play Store.
Abu Na Hudu: Kiyaye saka waya a kan Katifa domin Katifa ita ma tana Consuming ɗin Zafi. Lallai duk abinda zai saka waya ɗaukar zafi zai zama ana sassauta aiki dashi.
Abu Na Biyar: Kiyaye barin wayar a caji lokacin barci, domin a wannan lokaci wayarka zata cika baka ma san ta cika ba. Wannan zaike saka batirin ka Over Charge, wanda hakan ka iya jawo kunbure war batiri, a kiyaye da zarar waya ta cika takai %100 a cire ta a Charge.
Wannna kaɗan ne daga cikin hanyoyinnrage shan Caji.
Domln karin Bayani Za'a iya tuntubar mu ta wannan Email address din naKasa👇
basirusigau@gmail.com.
basirusigau@gmail.com.
Tags:
Yanar gizo