Hankula Ya Tashi | Yan bindiga sun sake kashe sojojin Nijar 89

A Nijar 'yan kasar ne ke ci gaba da alhinin mutuwar sojoji 89 da 'yan bindiga suka kashe a harin da suka kai Shinagodarar mai nisan kilomita 15 da iyakar Mali. Wasu 'yan kasar kuma na cikin bakin cikin yadda gwamnati ba ta dauki wannan babban rashi da muhimmanci ba, tare da yi wa jana'izar sojojin rukon sakainar kashi. Ana zargin gwamnatin da boye gaskiya lamarin da ya faru inda ta ambato sojoji 25 da cewa sune suka mutu.

Sai dai ganin yadda 'yan kasar suka yi nuna rashin jin dadi, tilas gwamnatin ta tabbatar da cewa sojoji 89 ne suka mutu. Wani da ya rasa dan uwansa ya ce '' kirga gawar sojoji 89 da aka kawo su, iyaye da 'yan uwa su na ta kuka kuma cikin sojojin da suka mutu akwai kanina da ban gane shi ba, don yawancin su ba a gane fuskokinsu, ko sunayensu saboda abin babu kyau.

Amma abin tashin hankalin shi ne akwai wadanda suka zo duba gawar 'yan uwansu, sai dai tuni an binne su. Hakan na nufin sai dai su yi zaman makoki, ba su da sahihin bayanin yadda 'yan uwansu suka mutu.'' Wasu dai sun zargi gwamnati da kokarin rufa-rufa kan mutuwar sojojin, ba a ayyana zaman makokin kasa kamar yadda aka saba ba.

Haka kuma jana'izar da aka yi wa sojojin babu wani jami'an gwamnati ko 'yan siyasa da suka halarta, kamar yadda aka yi lokacin jana'izar sojoji 71 da suka mutu a watan Disambar bara, da aka yi musu jana'iazar ban girma.

Yan Nijar sun koka kan yadda babu wani alamu na alhini da da kafafen yada labaran kasar suka sanya, hasalima sun ci gaba da shirye-shiryensu kamar yadda aka saba. A bangare guda kuma 'yan siyasa sun ci gaba da taruka da shagulgulan da suka saba, tamkar babu abin jumami da kasar ke ciki. Sai daga bisani ne gwamnati ta fitar da sanarwa, a ciki ta bayyana alhinin mutuwar sojojin, tare da ayyana zaman makokin kwanaki uku da za a fara daga ranar Litinin.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post