
Daga -Idishia Jos.
Kayi Addu'a a mamaci kamar kana yuwa kanka yazo cewa bama kama bane kana yiwa kanka ne, mamaci ya zamo kamar sila ne na kai ka samu wani gafara da rahma sakamakon abinda zaka yi masa na addu'a don haka ko wani Abu na sadaka. Don haka abinda zanyi magana a yanzu duk wanda iyayen sa suka rasu to ya sani cewa akwai hakki mai girma a kansa. Musamman ita Uwa Da Uba wanda suka sha wahala akan mutum to kada ya zamo wani abu mai rudarwa ya rudar da mutum.
Ya kamata ace kullum kayi Sallah kada ka tashi sai ka musu addu'a, in zai yuwu ma in zaka iya duk wani motsi ka tuna dasu ka musu addu'a to ba zaka sauke hakkin su ba. To, amma in kayi kokari duk wani sallah da zakayi ko Sallah 5 din nan akalla Kulhuwallahu 3 din nan kace Allah ya kai lada zuwa ga kabarin mahaifiyata ko mahaifina a Kullum azahar la'asar magriba isha Asuba ya zamo cewa muna yiwa iyayen mu addu'a.
Shehin Malamin ya kara da cewa; Mun sha bayanin Mutum zai iya zamowa mutum kirki da iyayen sa amma bayan sun mutu, sai a rubuta shi cikin masu sabawa iyaye saboda mai ? Saboda ya manta da su. To, muna fatan ya zamo kada mu zamo daga cikin masu mantawa da iyayen su, kada mu zamo masu mantawa da 'yan'uwansu.
Kuma ya zamo ana Sadaka, kayi Sadaka kace ladan Allah ya kai ga Iyayenka, akwai Sallah da ake yi ga iyaye zakayi sallah da rana raka'a 2 Fatiha, Inna Anzannahu, a raka'an farko kenan. Sai Fatiha da Inna A'adaina Kalkausar, bayan kace Assalu Alaikum sai kayi Salati ga Annabi kace Allah ya kai ladan zuwa kabarin Mahaifiyata ko mahaifina.
In kuma 'Dan ka ko yarka ta rasu, ko 'ya'yan ka wannan karatun raka'oin su kaza karanta a sallah da zaka musu raka'a 2 amma shi ba'a yinsa sai da dare na yara kenan. Kuma jifa-jifa ana yin sadaka da iyaye. Manzon Allah (S) yayi mafarki da Ja'afar Dayyar da kuma Abbas ya gansu a aljanna cikin Ni'ima sai ya tambaye su wani Abu ne mafi daukaka darajan mutum a lahira? Sai suka ce mishi abu na farko shine salatin Annabi (S).
Don haka mu yawaita Salati muce Allah ya kai wa iyayenmu a makwancin su. Sannan suka ce abu na biyu wanda suke daukaka darajan mutum a lahira son Amirul-Muminin Imam Aliyu (As). Wanda Manzon Allah (S) yake cewa ba mai son Ali sai Mumini ba mai kin Ali Sai munafiki. Abu na 3 shine suka ce shayar da Ruwa, ka sayi Ruwa koda "Pure Water" ne ka samu wasu bayin Allah ka basu su sha.
Sannan kuma daga cikin Hakkin iyaye akwai ziyarar Makabarta, bawai daga anje an binne shikke nan ba a'a kamar yadda in suna raye kai ma kana raye in baka zuwa wajen su Yaya kake gani! Zasuyi farin ciki da kai ? To, haka ma in basa raye baka ziyartarsu ba za su yi farin ciki da kai ba. To, idan ma baka san inda kabarin iyayen ka suke ba, to ka ZIYARCI kabarin wani bawan Allah sai ya zamo kayi ziyara Allah zai sadar musu da shi.
Alhamdulillah Allah ya mana baiwa da Malam Ibrahim Zakzaky da ya tabbatar damu akan wannan turba din.
Yanzu zamuyi addu'a ga mahaifiyar Idris HAJARA Allah (T) ya jikanta ya GAFARTA mata, ya haskaka makwancin ta, ya jaddada Rahma ga ruhinta, ya sadar da ita ga Sayyida Fatima Azzahara (As), dama iyayen mu gaba ki daya dama dukkan wanda suka gabace mu. Malam yayi wannan jawabin ne jiya bayan kammala Du'a'ul khumail tare da Addu'a cika Shekara Daya da rasuwan mahaifiyar Idris (-Idishia Jos. )
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga

Tags:
Jawaban Malamai