General Suleimani yayi shahada a sakamakon harin da Amurka ta kai mashi…


--Idishia Jos. 

 Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Da safiyar yau Jummu’a ne 3 ga watan Janairu 2020 babban kwamandan sojin rundunar Qods ta Iran General Suleimani yayi shahada sakamakon wani hari da Amurka ta kai musu.

Rahoton talbijin na Press Tv ya nuna cewa shi General Suleimani yayi shahada ne tare da Abu Mahdi al-Muhandis wanda shine na biyu a cikin manyan jagororin rundunar Hashdu Sha’abi na Iraki.


An kai wannan mummunan hari da sojojin Amurka ta jirage masu saukar ungulu a Bagdad inda suka sami wadan nan manyan kwamandoji.

A labarin da aka samu yanzu haka a kasar Iran din an bada hutun ayyuka na na tsawon kwanaki Uku. A cikin ta'aziyya da Sayyid Ali Khamene'i ya aika wa mutanen Iran yana cewa; Daukan fansa mai tsanani yana jiran wadanda suka aikata wannan aiki.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post