Gajeren tarihin harbo jiragen
saman fasinja a duniya
daga shekaru 50…..
A shekarar 1974 Turkiyya ta taba harbe
jirgin ruwanta mai dauke da sojojinta guda
350 kuma ta kashe sojoji guda 70 a ciki
bisa kuskure a yaqin Cyprus.
Japan ta taba harbo jirgin saman Russia
mai dauke da fasinjoji 269 kuma duka ta
kashesu,amma ba su yi magana a
gwamnatance ba saida akai shekaru 10
dayin abun.
Sannan Ukraine din ta taba harbo jirgin
Russia har wala yau, ta kashe mutane 78
amma ba’ai magana a gwamnatance ba
sai bayan kwana 8 da faruwan lamarin.
America ta taba harbo jirgin fasinjojin Iran
daya nufi Dubai wanda yake dauke da
fasinjojin sama da 240, daga ciki 66 duka
yara ne qanana ba wanda ya tsira a cikin
jirgin kuma America bata nemi afuwan Iran
kan haka ba, hasalima captain din da ya yi
wannan barnar qara masa girma aka yi!
A 2020 Iran tayi kuskuren harbo jirgin
Ukraine mai dauke da fasinjoji 176 saboda
barazanar yaqi da suke neman shiga da
USA a lokacin, kuma 84 a cikin fasinjojin
Iraniyawa ne, Iran ta karbi kuskurenta
kuma ta yi ta’aziyya ga iyalan wanda abun
ya shafa sannan ta dauki nauyin diyyar
hasarar rayukan da aka yi.
Tags:
Labaran Duniya