*GAGARUMIN GANGAMIN MANYAN MALAMAN HAUZA DA DALIBAI NA YANKIN TEHRAN-IRAN*


Karkashin kulawar Ayatullahi Aliy Akbar Rashad._








  *Wan nan wani sako ne na Musamman da yafi shafar 'yan'uwa almajiran Sayyid Zakzakiy (H)*

Laraba:
5/Jimada Ula/1440.
11/10/1398 Shamsiy
1/1/2020. Miladiy,

Kamar yadda aka saba gabatar da Tarurruka, Gangami da sauran Zamammaki don kiran a saki Jagoran Harkar Musulunci na Najeriya Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) a Jamhuriyyar Musulunci ta Iran, kamar kodayaushe  haka dimbin Malamai da Dalibai ne na yenkin Tehran, suka gabatar da Taro danagane da halin da Sayyid din yake ciki .

Taron ya samu halartar _Sayyida Suhailat Ibrahim Zakzaky_

    GABATARWA.

    Malami mai gabatarwa ya bayyana cewa, taron yana kunshe da Wata farkawa ta Malaman Hauza, don nuna cewa Sayyid Zakzakiy (H) bashi kadai ba ne;  Maraji'ai,  Malamai, da Daliban Hauza, suna tare da shi.

   kasantuwar da basu da masaniya dangane da Malama (H), kuma basu san da'awar sa ba, amma yanzu sun fahimci cewa ashe shiukar da Imam Khomainiy (Qs) ya yi ce ta tsiro a Afika, har ta girma basu an kara ba, don haka bzasu bari Malam (H) ya zama shi kadai ba. Suna rokon Allah ya yafe musu kura-kuran da suka yi abaya, na rashin bibiyar lamarin sa.

  Mai gabatarwan wanda yake  Malami ne mai farin rawani, ya karanata Sakon gaisuwa da jinjina ga Jagoran duniya Sayyid Zakzakiy (H), -inji shi- a madadin duk Malaman Hauza na Yenkin  Babban birnin na Tehran, wadan suka halarta da ma wadan da wani Uzrin ya tsare su basu samu zuwa ba. *Dakin Taron make yake fal da Malamai masu rawani!.*

  JAWABIN SAYYIDA SUHAILA.

  Sayyida Suhaila ta gabatar da Malama Badiyyah, don ta yi bayani cikin Harshen Farisanci, game da hali da yanayin da su Sayyid (H) Suke ciki ahalin yanzu.

  Ganin ido ya tabbatar da Malamai "Sadat" watan Sharifai wadan da suka kai matsayin Ijtihadi da sauran manyan Malamai, wadan da suma Sun kai mukamin Ijtihai a tsarin Hauza, suna zubar da hawaye don yadda suka ji wahalar da Azzalumai suke ba dan'uwan su Malamin Addini Allamah Sayyid Zakzakiy (H) daga bakin Malama Badiyya.

   Alokaci guda Kungiyoyin Dalban Jami'a na Babban Birnin Tehran, suma suna can wani babban Dakin taro nasu, suna zaman nazari dangane da da'awar Jagora da matakan da Azzalumai da munafukan duniya suke dauka. Tunani suke da nazari akan cewa wai *meke faruwa ne Dawagitan duniya da munafukai suak lashi takobin sai sun ga bayan Sayyid Zakzakiy (H) da da'awar sa.*

*Ayatullahi Aliy Akbar Rashad (H) Tehran, ya  suffanta Malama Zeenah ta fuskacin dakekwa da Sayyida Zahra, yayin da ta dake ta kare Manzon Allah (saww), ya ce wan nan dakewar da Malama Zinah ta yi tare da Jagoran Addini Jarunta ce irin ta Sayyida Zahra (as).*

Ya kuma suffata su Sayyida Suhaila a wannan Jaular da suka gabatar, ta kusan mako guda, inda suka ziyarci kusan dukkan Fitattun Manyan Maraji'ai a Birnin Qom Al muuqaddasah zuwa Birnin Teharn, da cewa su ne Zainabawan wannan Zamanin, kamar yadda Sayyida Zainab ta yi Jaular yada mazlumiyar waki'ar Ashura, kuma aikin su ya nuna cewa har yanzu akwai zainabawa da kuma aikin Sayyida Zainaba (as).

JAWABIN DR. ALIY RIZA FANAHIYAN.

  Hujjatul Islam Fanahiyan, ya bayyana cewa, Rashin Taimakawa Sayyid Zakzaki ta fuskacin shimfida yanayin da zai tursasa Azzalumai su saki shi, zai iya jawo rushewar Nizamin Musulunci na Iran, wanda a halin yanzu yake da karfin gaske. Ya kara da cewa nuna halin ko - in - kula akan lamarin Sayyid Zakzakiy (H), zai iya jawoma dukkan kasashen Musulmi kaskanci da dawwama cikin danniyar kurayen duniya, masu rarraba duniya don su ci riba da kwashe arzikin kasashen Musulmi.

   Fanahiyan ya karanta wani sashe na fikirar Imam Komaini (R), wanda yake nuna wazifar Malamai da Daliban Addini, cewa wajibi ne su yi  tunani akan samuwar Babbar daular Musulunci ta duniya, dole ne karatu da nazarin littafai da fafutukar Gwa-gwarmaya da ake ta faman yi ayau, su maida hankali akan janye iyakokin da makiya suka shata, don rarraba duniya da zaluntar al ummar Musulmi baki daya.

   Shahararren Malamin Dr. Fanahiyan ya kara da cewa, a gaskiya mu daliban addini a kasashen Musulmi mun yi abin kunya sosai, ta yadda muka rabu da Shekh Zakzakiy (H) muka kyale shi, har takai yanzu gashi yana lunfashin da yayi kama da na karshe, yana neman ya yi bankwana da mu, dole ne mu farka mu yi abin da ya dace akan wan nan bawan Allah (Sayyed Zakzaky).

   Dr. Fanahiyan ya cigaba da cewa, ba dai-dai ba ne,  Daliban Addini su maida hankali kawai akan karatu da nada Rawunna, su kyale tafarkin muqawama bata da ma'aikata, ya ce ba daidai ba ne, Malamai su bar Sheikh (H), a matsayin cewa shi na Nigeria ne, wannan rashin fahimta ne, Sheikh Zakzaky ya fi karfin ace ma na Afrika ne, aikin sa na duk duniyar Musulunci ne, kuma ya wajaba ga Malaman duniyar Musulunci su farka tun kafin su rasa wanda ya kafa musu harsashen gini mai karfi, su taimaka masa, suma suyi aiki da wazifar su.

   An kammala Zaman tare da Yima Jagora addu'o' da Kuma jaddada kira ga Malamai da Dalibai da duk Al'ummar Musulman duniya da su tashi  tsaye da addu'o'i, da duk abin da zasu iya yi don ganin Jagora Sayyid Zakzakiy (H) ya samu Yanci.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post