Zalinci:/ Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufa'i Na Yunkurin Yanke Hukuncin Kisa Ga Sheikh Zakzaky.


Daga Wakilin Shafin Mu -Idishia Jos.

Ma`asumah nigeria news 📰 update

A sanyin safiyan yau Juma'a Labarun gidan radio Liberty Kaduna  ya labarta wani labari wanda sanarwan ce ta fito daga fadan gwamnan Jihar Kaduna, akan cigaba da tsare Sheikh Zakzaky da matarsa malama Zeenat da kuma hukuncin da zasu aiwatar a Kansu.

Kwamishinar shari'a ta jihar Kaduna, Jastis Aisha Dikko, tace makomar shugaban kungiyar musulmai mabiya akidar shi'a, Malam Ibrahim El-Zakzaky ta dogara ne a hannun kotu.

Kwamishinar ta sanar da hakan a ne wata takarda da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce gwamnatin jihar Kaduna bata da nufin janye zargin da take mishi, amma ta bar kotu ta yanke hukunci. Ta ja kunnen cewa wannan shari'ar kada ta zamo wani abu da za a yi kamfena kafafen yada labarai ko kuma wajen tursasawa kowacce iri.

 A cigaba da bayanin dalilin da yasa gwamnatin jihar ba za ta saki shugaban IMN din ba, Dikko ta jaddada cewa El-Zakzaky da matarsa Zeenat na fsukantar zargi ne na laifuka takwas, wadanda suka hada da kisan kai wanda hukuncinsa kisa ne.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post