🇳🇬Ma'asumah Nigerian News Update
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin hirar da aka yi da shi a wani shiri na kai tsaye a Kaduna kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Mr El-Rufai ya ce gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakai a kan shugaban na Shi'a saboda ne saboda wahalhalun da ya jefa mutanen Kaduna a ciki.
"Mun yarda (makomar shi na hannun mu) amma da gyara. Makomar El-Zakzaky baya hannun gwamnatin jihar Kaduna sai dai yana hannun babban kotun jihar Kaduna."
Gwamnatin tarayya ba ta kai El-Zakzaky kotu ba. Gwamnatin tarayya ta tsare shi na a Abuja bayan afkuwar rikicin.
"Da ya ke tsare a Abuja, mun zauna mun gudanar da bincike a kan barna da laifuka da take hakkin mutane da shi da mabiyansa suka aikata a shekaru 30 da suka gabata a Zaria.
"Bayan kammala binciken, mun bukaci gwamnatin tarayya ta bamu shi don su gurfanar da shi a kotu a Kaduna.
"Duk masu neman a saki El-Zakzaky da gwamnatin tarayya su ke. Tunda muka tsare shi babu wanda ya ce mu sake shi.
"Kuma ba za mu sake shi ba har sai kotu ta wanke shi.
Babban kotun jihar Kaduna ce ta bayar da umurnin tsare shi a gidan gyaran hali na Kaduna.
"Shi ne ya nemi SSS su rike shi a maimakon gidan gyaran hali. Idan mutum yana jiran shari'a, a gidan gyran hali ya kamata ya jira. Amma shi ya zabi a ajiye shi a wurin SSS saboda baya son ya wahala.
"Tunda SSS ta rike shi ba tare da umurnin kotu ba, lauyoyin mun nemi umurni daga kotu don mayar da shi gidan yari.
"Da muke magana a yanzu, Sheikh El-Zakzaky da matarsa suna gidan yarin Kaduna kuma za su cigaba da kasance a can har sai an kammala shari'a.
"Ba mu san lokacin da kotu za ta yanke hukunci ba amma ba za mu sake shi ba saboda laifukan da shi da mabiyansa suka yi wa mutanen Kaduna.
"Idan kotu ta wanke shi, ba mu da zabi. Amma ba za mu sake shi ba komin irin matsin lambar da za ayi mana a gida da kasashen waje...
"Su na bata lokacin su ne. Idan dai har ni ne gwamna, ba zamu taba auren El-Zakzaky ba har sai an kammala shari'arsa. Amma duk abinda kotu ta zartar, zan aiwatar
Mai karatu komai nene ra'ayinka dan gane da wannan maganar
Daga Wakilinmu
MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com
Tags:
Jagoran Gaskiya