*Maasumah Nigerian News update*
DUKKAN DAN-UWAN DA YAKE SAURARON JAWABAN MALAM ZAKZAKY(H) BA ZAI SAMU MATSALAR SAITI BA...!!!
...Umar Hassan Gololo...
Akwai jawaban Malam Zakzaky(H) na munasabobi da yawan gaske, akwai wa'azin dare, akwai jawaban rufe mu'utamar na garuruwa dabam-dabam, akwai jawaban ganawar Malam Zakzaky(H) da 'yan-uwa khassa da ama....
Ga uwa-uba tafsir da karatun Nahjul-Balagha,ga jawaban zaman makokin Ashura da jawaban Mauludin Annabi Muhammadu(S) dana Iyalansa(AS),a matsayinka na Almajirin Malam Zakzaky(H) irin wadannan jawaban guda nawa ne a computer ko wayarka.?
Shin sauraron jawabin jagora ga mabiyi ba waraka bane.?
Idan baka saurari jawaban jagoranka ba jawaban wa zaka saurara.?
Ni na tabbata idan kana sauraron jawaban Malam Zakzaky(H) domin neman mafita insha Allahu Ta'ala babu wani santsin da zai ja kafarka ballantana ka Fadi warwas......
Allahu Ta'ala ka kunyata makiya Malam Zakzaky(H) ka kaskantar dasu ka gaggauta kwato Mana shi daga hannun azzalumai alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi......
Tags:
Makaranta