Domin Kada Imam Ali (As) Ya Rasa Sallar Asuba Allah ya turo Mala'ika Jibril Da Ruwa Daga Aljanna!!!


Wa Allah (swt) ya daraja da irin darajar da yayi maka Bayan Manzon Allah ya Ali!..

Ku karanta wannan kissar kuji meya faru a wani dare ko kuce wajen gab da asubahi.

Khawarizmi ya ruwaito daga Anas Bin Malik cewa; "Wata rana Manzon Allah (S) ya kira Abubakar da Umar ya umurce su da suje su tambayi Ali Abinda ya faru jiya da daddare."

Manzon Allah da ka kansa yana biye dasu a baya, Anas yace; "Nabi Abubakar da Umar zuwa gidan Ali. Yayin da Imam ya fito daga gidan sa ya tambayi Abubakar: "Shin wani abu na musamman ya faru jiya da daddare ne?

Abubakar yace; "Babu wani abu mai daraja da aka ambata! Manzon Allah ne ya turo mu wajen ka muzo mu tambayi abinda ya faru jiya da daddare.  Ana haka saiga Manzon Allah (S) ya kariso yace wa Ali gaya wa wadannan mutane abinda ya faru daren jiya.

Ali ya bada amsa da cewa; "Ya Ma'aikin Allah! Bana da kwarin guiwa akan wannan lamari. Manzon Allah yace, fada wa wadannan mutanen domin Allah baya jin shakkar bayyana gaskiya.

Imam Ali yace, "Lokacin dana je domin yin alwalar Asuba, ban sami ruwa ba, saina fara tsoron kada inzo in rasa Sallah ta. Sai na tura Hassan Da Al-Husain su debo ruwa amma, sai suka dauki tsawon lokaci basu dawo ba.

Sai naji tsoro da tashin hankali. Cen sai naga rami ya bayyana a  saman rufin daki, saboda haka naga Mazubin ruwa (Zamu iya cewa Bokiti) nannade da kyalle. Sanda bokitin ya sauko kasa saina cire kyallen na samu bokitin nan cike yake da ruwa nayi alwala tare da  wanke jiki na kammala Sallar Asubahi dina.

Da bokitin da kuma kyalle suka koma zuwa saman rufin suka bace shima Ramin ya rufe."

Manzon Allah (S) yace; "Bokiti da kyallen daga gidan Aljanna suke, shi kuma ruwan daga koramar gidan Aljanna. Ya Ali! Waye zai wuce ka, alhali Mala'ika Jibril dakan sa jiya yayi maka hidima."

Don ƙarin bayani a duba, Kashful Yaqin, Shafi na 301. Al-tara'if, Shafi na 85.
Al-Saqib lil Manaqib, Shafi na 272.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post