TUNATARWA:/ dole a mutu ko aji rauni wato ciwo kafin yin nassara!!!

SHEIKH IBRAHEEM ZAKZAKY {H}
                                   

                                       @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SAI DAI KU KUNA DA KYAKKYAWAN FATA

Ita sunnar Allah ba ta canzawa kuma ba a yi mata kwaskwarima , yadda ya tsara al'amarinsa dole ya kasance  haka za ayi kafin ayi nasara ko kafin taimakonsa (T )ya zo .

An kashe sahabban Manzon Allah (S.A.W.W ), wasu sun rasa bangarorin jikinsu , wasu kuma an raunata su , amma a haka suka jajirce har taimakon Allah yazo musu .

Bambancin da ke tsakanin musulmai da kafirai shine, su musulmi suna tsammanin samun rahmar Allah ko da an kashe su , su kuma kafirai ba su da wannan tsammanin, amma hakan bai hana su su riqa tsokanar musulmi ta hanyar kai nusu hari ba.

Allah (T )na qarfafar bayinsa muminai  ba su labarin bambancin da ke tsakaninsu da kafirai yayin haduwar su (physical comvert ), yana cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KUMA KADA KU SASSAUTA A CIKIN NEMAN MUTANE (kafirai yayin da suka kawo muku hari ), IDAN KUN KASANCE KUNA JIN ZOGI (pain )(daga abinda su kayi muku ), TO, LALLE SU MA SUNA JIN (irin wannan)ZOGI KAMAR YADDA KU KE JIN ZOGI. KUMA KUNA TSAMMANIN (samun rahma)DAGA ALLAH , ABINDA (su kafirai )BA SU TSAMMANI . KUMA ALLAH YA KASANCE MASANI MAI HIKIMA.‘’

(NISA'I:104)

Wannan aya na nuna mana ne cewa kada mu kasance masu tsoro da karaya kan abinda zai same mu daga kafirai ko azzalumai kan hanyar Allah, domin duk irin abinda mu ke ji su ma suna jin irinsa, kuma nasara da rabauta ce a gaban mu cikin abinda zai same mu, su kuma ba su da wannan fata.

Daga wakilamu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

          08126385470

~10th January , 2020.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post