Dandalin Matasan Yankin Jos Sun Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani!!!

 Ma'asumah Nigerian News Update

 A shekaran jiya Juma'a 3/January/2020 ne yan uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) na Yankin Jos wanda ya hada yankunan Keffi, Saminaka, Jos, Lafia, da Doguwa suka shiga Taron Karawa Juna Sani (Mu'utamar) na yini biyu wanda aka gabatar a garin Ramin Kura na Da'irar Saminaka. Inda Malamai da yawan gaske suka gabatar da jawabai akan Maudu'ai daban-daban. Inda take Taron ke nuna cewa shine "Gina Shaksiyyar Dan Uwa Matashi A Tafarkin Gwagwarmaya".

 Inda a yau Lahadi 5/1/2020 Hujjatul Islam Wal Muslimin Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos ya rufe taron bayan gabatar da Tamsiliyya da sauraron Baitoci daga Sha'irai. A cikin jawabin nasa Sheikh din yake cewa "In yan uwa matasa suka tsaya suka natsu akan tafarkin da jagora ya Dora mu, toh lallai za a cimma wata manufa nan gaba, a bisa bincike da nazari da muka yi mafi yawan matasa basu fahimci hakikanin Tafiyar Malam (H) ba".

 Sannan kuma ya kara da cewa "Saboda rashin wayewa na wasu 'yan uwan zaka ga wasu sun ci gayu kaman wayayyu ashe ba haka bane babu sakafa a tattare dasu. Ance wadansu sunje ziyara prison sai aka ga sun tsaya a kofar prison wai suna selfi. Sai aka kamasu, wai kuma da aka tambaye su meye suke yi sai suka ce mun zo ganin Dan uwanmu ne. Har ma aka ji suna waya da wani aka tambaye su dawa kuke magana suka ce da wani Dan uwanmu ne da yake a prison din. Sai aka ce ku bani number shi kuma suka bayar wai a haka kuma su Almajiran Sayyid Zakzaky ne". An kammala Taron lafiya kamar yanda aka fara lafiya.

Daga wakilanmu na Saminaka.
                Tare da,
Ibrahim Almustapha Saminaka
             5/January/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post