Yazo a ruwaya daga Sa'ad Bin Abdallah ya ruwaito daga Ibrahim Bin Hashim shi kuma ya karbo daga Abdallah Bin Al-Mugheira daga Abu Abdallah (As) yace; yayin da Zulayha ta bukaci ayi mata izini taga Yusuf (As).
Su suka ce mata muna tsoron gabatar dake a gabansa duba da abinda ya auku tsakanin ki dashi (ta sa an saka shi a kurkuku). Sai tace; "Bana tsoron wanda yake tsoron Allah."
فلما دخلت قال لها: يا زليخا مالي أراك قد تغير لونك؟ قالت: الحمد هلل الذي جعل الملوك بمعصيتهم عبيد، وجعل العبيد
بطاعتهم ملوكا قال لها: ما الذي دعاك يا زليخا إلى ماكان منك؟ قالت! حسن وجهك يا يوسف فقال كيف لو رأيت نبيا يقال
له محمد يكون في آخر الزمان أحسن منى وجها وأحسن منى خلقا واسمح منى كفا. قالت: صدقت، قال وكيف علمت إنى
صدقت قالت: النك حين ذكرته وقع حبه في قلبي. فأوحى هللا عز وجل إلى يوسف إنها قد صدقت وانى قد أحببتها لحبها
محمدا، فأمره هللا تبارك وتعالى ان يتزوجها.
Yayin da aka mata iso zuwa gare shi Sai Annabi Yusuf yace da ita, "Yake Zulayha me ya same ki naga duk kalarki ta cenja?
Sai tace; "Tsarki ya tabbata gun Allah wanda yake mayar da mai mulki ya koma bawa bisa kin bin umurnin sa, ya kuma mayar da bawa ya zam sarki domin biyayyar da yake ga Allah madaukakin sarki".
Sai Yusuf yace me ya kawo ki gareni, bayan duk abinda ya gudana daga gare ki? Sai tace; "Kyawun fiskarka ya kai Yusuf! Sai yace mata, Ya zata kasance kenen inda zaki ga Annabin Allah da ake Kira da Muhammad, wanda zaizo a karshen zamani, ya fini kyawun fiska, ya fini dukkan kyawu, kuma shine wanda yafi kowa duniya da lahira, ga yawan kyauta?
Zulayha tace; Ka fadi gaskiya, domin daka ambata min shi saida naji matuqar soyayyar sa a zuciya ta.
Sabida haka, Allah mai girma da daukaka yayi wa Yusuf wahayi yana cewa; ta fadi gaskiya, sabila da soyayyar ta ga Masoyina Muhammad nima ina sonta. Don haka Allah mai girma da buwaya ya Umurci Annabi Yusuf da ya auri Zulayha.
Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad.....
Don karin bayani a duba, Ilal Al-Sharae, Mj na 1, Jz na 47, Hadisi mai lamba 2.
🇨🇮 Ma'asumah Nigerian News Update, tare da Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ.
Tags:
Taskar ilimi