Da Dumi-duminsa: An Sake Yi Wa Sansanin Amurka Ruwan Rokoki A Iraqi

Daga wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.


Labarin dake fitowa daga kasar Iraqi na nuni da cewa wadansu rokoki sun sake dira a sansanin sojojin Amurka dake Arewancin Baghdad dake Iraqi. Sansanin dai da rokokin ya sauka sojojin Amurka ne ke zama a wurin.

Hukumomi a kasar sun ce akalla sojojin Iraqi hudu suka jikkata daga harin.

Sai dai wata majiyar soji a yau Lahadi ta shaidawa kafar watsa labarai na AFP cewa mafi yawan sojojin sama na Amurka dake sansanin na Balad kilomita 80 dake arewacin Baghdad tuni suka bar sansanin.

Kanal  Mohammed Khalil, wani jami’in dan sanda dake Arewacin Iraqi dake yankin Saladin, ya bayyana cewa; rokokin dai sun sauka ne a cikin sansanin, a yayin da wasu rokokin suka sauka a bakin kofar shiga sansanin.

“Sojojin Iraqi uku wadanda suke gadi a kofar shiga sansanin sun jikkata sakamakon wannan harin.” In ji shi.

Ya zuwa hada wannan rahoto babu wanda ya dauki alhakin kai harin a yayin da ake tsaka da sa’insa da tankiya tsakanin Amurka da Iran a tsawon mako biyu.

A makon da ya gabata ne, kasar Iran ta harba makamai masu linzami a sansanin sojin Amurka mafi girma dake Iraqi, hakan ya biyo bayan kisan gillar da kasar Amurka ta yiwa Kwamandan Iran din Janar Qasseem Soleimani a wani harin sama a Baghdad

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post