@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HALAKARWAR ALLAH NA NAN TAFE A KANKU
Babu wata gwamnatin kafirci ko ta zalunci wacce tayi nasara kan Manzannin Allah (A.S )ko kuma akan Mujaddadai wadanda Allah ya tayar don jaddada addininsa na gaskiya .
Ko da kuwa tarihi ya kawo cewa an kashe Annabawa (A.S )masu yawa ba hakan na nuna cewa anyi nasara a kansu bane , a'a , sune su kayi nasara don sun koma ga madaukakiyar makoma ce ga Allah . Ita gwamnatin kafirci da zalunci ne su kayi hasara da halaka , domin qarshen su ba ya taba zama alkhairi .
Allah madaukaki mai ikon akan dukkan halittunsa na cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ LALLE NE WADANDA SUKA KAFIRTA DA AYOYIN ALLAH , KUMA SUNA KASHE ANNABAWA BA TARE DA WANI HAQQI BA, KUMA SUNA KASHE WADANDA KE UMARNI DA YIN ADALCI DAGA MUTANE, TO, KA YI MUSU BUSHARA DA AZABA MAI RADADI .‘’
(AL-IMRAM:21)
Babu wani mai yin kira na gaskiya da yazo ba tare da azzaluman mahukuntan zamanin sun yi qoqarin halakar da shi ko korarsa ko kuma gargadinsa kan cewa ya dawo cikinsu ta hanyar yi masa barazanar kisa ba , sai dai ba sa yin nasara ta hanyar wannan barazanar ta su , sai dai busharar Allah a kansu cewa zai halakar da su.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KUMA WADANDA SUKA KAFIRTA SUKA CE WA MANZANNINSU, ‘’ LALLE NE MUNA FITAR DA KU DAGA QASARMU, KO KUMA HAQIQA KUNA KOMAWA CIKIN ADDININMU.‘’ SAI UBANGIJINSU YAYI WAHAYI ZUWA GARE SU, ‘’ LALLE NE, MUNA HALAKAR DA AZZALUMAI .‘’
(Sutatul-Ibrahim:13).
MUJE ZUWA DAI, LOKACI ZAI YI HALINSA .
Daga wakinmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda .
08126385470
~12th January , 2020.