Rahotani daga garin Gamboru; gari kan iyakar Nijeriya da Kamaru a jihar Borno, sun bayyana cewa sama da mutane 35 ne suka rasa rasa
rayukansu ta dalilin tashi wasu ababe masu qarar gaske, wanda a ke kyautata zaton bom ne.
Al’amarin ya faru da misalin qarfe 4:00 na yammacin ranar Litinin din da ta gabata, lokacin cincirindon jama’a, a kan gadar bakin kasuwar garin. Wani ganau a wurin da bam din ya tarwatse, Malam Ahmad Musa, ya shaidar da cewa tashin bam din ya yi kaca-kaca da jinin jama’ar da lamarin ya rutsa da su a ilahirin bakin gadar, abin babu kyaungani.
Ya ce, “Kawai sai qarar fashewar wani abu; mai qarar gaske a wajen, kafin mu fahimci abinda ke faruwa, wanda da idona na ga bangarorin jikin jama’a zube a qasa, yayin da qananan yara sai kukan neman dauki suke. Al’amarin ya girgiza hantar jama’a”.
Da hannuna na qirga gawawakin jama’a kimanin 32 wadanda tashin bam din ya rutsa dasu. Kuma abin ya faru ne kan gadar Fotokol wadda take kan iyakar Nijeriya da Kamaru.
Shima wani bawan Allah wanda yana wajen bam din ya tarwatse; Malam Ali Mohammad, wanda ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala tantance sanin abinda ya haifar da tashin bam din ba.” Haka kuma ya bayyana cewa, mutane da dama sun samu raunuka, wanda mafi yawan su mata da qananan yara ne. Sannan kuma
tashin farko mun kwashe mutane 35 zuwa asibiti, ya qara da cewa kuma mutane da yawa sun gamu da raunuka.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates tare da --Idishia Jos.
Tags:
Labaran Duniya