Ba`a Taɓa Samun Shaheedi A Mafara ba ko Acikin Jihadin Shehu ɗan Fodiyo, Sai da Wannan Lokaci da Gwagwarmayar da Maulana (h) ke yiwa jagoranci!!!



–Mlm Abbakar Nuhu Talatar Mafara

Wakilan Ma`asumah Sunje ta`aziyyah Ga Wakilin Yan uwa na mafara dana Birnin Tudu,  tare da Iyayen Shaheed ayau Assabar

Da yammacin Yau Assabar ne  18-jan-2020 Wasu daukacin Wakilan ma`asumah Sukayi tattaki Domin jajantawa Iyayen shaheed tare Da wakilin  yan uwa na mafara mlm Abubakar Nuhu talatar mafara,


A yayin Ziyarar inda malamin yayi gwala-gwalan bayani akan Shidan da aka samu a Mafara,  da kuma  shi kanshi  Shaheed Ishaq Muh`d Suleman,  Kuma yatabo Bayanin yadda Waki`a ta farko yadda ta riskesu a mafara da yadda aka samu shaheedin farko a mafara wanda ko lokacin jihadin Shehu usman dan fodiyo ba`ataba samun shahidi a mafara ba…. 
Malam yatabo wani janibi na maganar da aka kaiwa su Sayeed ziyarar suka ce a wani lokaci bayan waki`ar zariya..

Malamin yayi zantuka ga Yan media da kuma karfafawa tare da Addu`a ga wannan shafin na Ma`asumah da wakilansa  ,
Daga bisani aka rufe da addu`a… 

Wakilin  mu mai kula da gidan. Radio MA`ASUMAH RADIO Conred Nazeer Sa`idu gusau Ya Dauki sautukan a audio kuma insha Allah  zakuji Shirin Kai ziyarar da zantukan. Nan bada dadewa ba

Akwai kuma firar da wakilanmu sukayi da wakilin yan uwa na birnin tudu inda mahaifar shaheed Ishaq take da kuma wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar shaheedin wanda haka yakamata ya zama abun koyi ga sauran yan uwa…
Abun sai dai kun saurara..

Bayan wannan ta`aziyya ta rashin wannan wakili namu wakilanmu  sunkoma garuruwansu cikin Alhini da jajantawa junansu game da wannan rashi da yazo mana…

Allah ya karbi shahadar sa ya bamu irin tasa Alfarmar sayyadah ma`asumah (s).

Ga wani bangare na ziyarar mlm Abbah acikin  Hotuna
👇👆👇👇👇




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post