Zamanki mai hadafi akan abinda kike yi shi zai ke ƙarfafa miki guiwa da ƙara ƙaimi akan zama lamba ɗaya cikin ajinku baki ɗaya. Hakan zai baki damar jan ragamar ƴan uwanki mata ta yadda ko wacce zata ke nemanki koda ke baki nemeta ba kinga kin fara nasara a tafiyarki.
-Domin ma'abocin addini ko ina ka gansa zaka ga addini yake, domin lamuransa gaba ɗaya addini ne. Yanzun tunda kin sami nasarar mallakar zuciyoyin ƴan uwanki zaki iya bada shawara a ɗauka, kinga daga nan zaki iya 'Organising' da basu shawara don kafa Qungiyar na iku-iku da zakuke warware wa kanku matsaloli da suka shafi karatu da sauran abubuwan da ya shafi kashin kanku.
-To, wannan dama ce babba don isar da saƙon addini domin daga haɗa gungu da yakai biyu zuwa uku saiki ga ke kanki wataran kin zama uwar gayya mai faɗa aji da kuma bada shawara abi. Tanan zaki ƙara da nuna musu addini da basu shawarwari akan abinda ya shafi Aƙlaq da kyautatawa juna da ziyarori ta yadda kowacce nace ko namiji sukaji labarin 'Group' ɗinku saisun so kasancewa cikinku, daga nan za'a sami mutane masu taqwa da taka tsantsan a lamuran addini mai makon da da kike ke kaɗai.
-Da yawan lokuta abunda ke saka ƴan uwanmu mata cikin halaka a Jami'o'i shine rashin fahimtar karatu domin ko yawancin mutane akan basu 'Addmission' ne na sashin da basu da masaniya akansa, sai su fara neman mai yi musu karatu ko ince 'tutorial' a gefe guda kuma shi yana ganin ya sami dammar juya ki tunda kece mai buƙatuwa gareshi, ta yadda in kinaso yaci gaba da koya maki karatu zaki karɓi ƙudirorinsa.
-Lallai, yana da gayar muhimmanci mu kula da masu farautar imaninmu, a matsayinki na mai ilimi kuma shugaba a cikin matan Jami'a kina da damar tallafawa ƴan uwanki ta hanyar haɗa su da mutanen kirki da kuma ƙawaye masu ilimi ta yadda zakuke samun lokutan karatu yaku-yaku, kinga baku kusanci mutanen banza ba balle su lallata muku tunini duba ga rauni irin na ƴan uwanmu mata.
-Anan ƴan uwana maza suma akwai rawar da suke bari basu takawa wajen jawo ƴan uwansu mata a jiki da kara saita su duk lokacin da suka gan suna kauce hanya, kana iya inka gan ƴar uwa tana kusantar wanda baka yarda dashi ba kake bata shawara ka ɗauka kamar ƴar uwarka ta jini kaji zaka iya bada ranka don kare mutuncinta, da kuma sama mata mutum na gari dazai ke koya mata karatuttukan da bata fahimta ba, amma na lura wasu samarin basa kusantar ƴan uwanmu Sistoci saidai kake ganinsu da Aaman mata wai a faɗarsu ƴan uwanmu mata suna da girman kai.
-Abinda ni na lura dashi shine girman kan da ake danganta musu ba girman kai sunansa ba, taka tsantsan ne ɗa tsantseni wajen kiyaye kai da ɓatattun ƴan uwa ko kuma ince jami'an sirri da aka saka su cikin ƴan uwa don bata tarbiyyarmu, masu son kusantar mata da soyayyar yaudara. Amma ka tsaya kai tunani komin girman kan mace matuƙar akan abinda zata karu ne, to, dakanta ma zatake binka kuma barinsu suna mu'amala da aama zai saka su iya faɗawa soyayya dasu, domin ita zuciya tana son mai kyautata mata ne, gashi ta sami wanda yake warware mata matsalolinta kai kuma gudunta kake.
-Inba mu taimaki kanmu da ƴan uwanmu ba wajen saita imaninsu ba me kuma zamuyi? Mu fahimci fa, da'awar addini da komi ta gida ake farawa mu koma tarihin Musulunci lokacun da aka aiko Manzon Allah (S) zamuga abu na farko da Manzon aka umurceshi yayi shine ya kira makusantansa, don haka duk wani gyara ko abinda zamu fara to, kada muke mantawa da ƴan uwanmu makusantanmu.
-Allah ya datar damu ya ƙara mana ƙaimi wajen yin addini da Iklasi ya bamu ikon sarrafa zukatanmu, ƴan uwa anan zan dakata saimun haɗu a ci gaban wannan rubutu.
ALLAH YA ƘWATO MANA JAGORANMU SAYYID ZAKZAKY (H) A HANNUN AZZALUMAI, YA BASHI CIKAKKIYAR LAFIYA DA NISAN KWANA.
┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

KARANTA WANNAN:- 'Yar Uwa 'Yar Jami'a Kashi Na Daya (1)