Ƴan Uwana Mata Ku Daina Saka Hotunan Ku a Social Media!!!




@Ma'sumah Nigerian News Update, Tare da Bin Haroun Sigau.

Kwana kin baya cen nayi wasu bayanai a harshen Turanci saina ga kamar akwai buƙatuwar Sistocinmu wanda turanci ke basu wahala suma su sami fahimtar wannan bayanai nawa.

-Idan Musulma taji ana cewa saka hotunanta a Whatsaap ko facebook yakan zama fitna sai ta fara musawa.

-Tana cewa amma wannan nice, kuma wannan fiskar mutane ke gani duk lokackn dana fita koda akan hanya ne.

Amma ga amsa bisa hakan.

-Abu na farko idan kika saka hotonki a Facebook ko Whatsaap kina haifar da fitina ga ƴan uwanki Musulmai, sabida bakya basu damar kaucewa matsanancin kallo da zai harfar musu da sha'awa koda ko kin saka Hijabi a hoton.

-Akan hanya kikan sami damar rage kallonki kamar yadda suma ƴan uwana maza suke kiyaya kallonsu gareki.

-Amma a Internet, ba haka abin yake ba ya bambanta sabida Namiji zaiji a sake yake ya kalli hotonki a duk lokacin daya so, Sabida kina yaɗa shi ga dukkan duniya ne.

-Yake ƴar uwa taya zaki bar wani cen ya sami damar kallon fiskarki, idonki da laɓɓanki da sauransu...

-Taya zaki bari idanunsu suita kallon jikinki? Ko wanne Namiji zaiga bashi da shamakin ya kalli hotonki ako da yaushe cikin kafar sadarwa.

-Ba tare da tunawa da Allah (T) da Imam Mahdi (Atfs) suna kallonsa ba.

-Lallai, yana bijerewa umurnin Allah, amma kiyi tunani! Wanene ya sakashi bijirewa umurnin?

-Abu na Biyu, a Facebook wani can baƙo zai iya downloding ɗin hotonki Ya aje a wayarsa ba tare da saninki ba koma ya saka a wanke mishi.

-Kiyi tunani! Zai iya amfani dashi don shirya ƙarairayi, koyin amfani dashi a kafafen sadarwar banza, koma wani kafar sadarwa da abinda ma yafi haka. Zasu iya Editin ɗinshi su saka a Internet sabida nishaɗi.

-Abu na Uku, kiyi tunani zunubai nawa zaki ɗauka ga duk wanda yai duba zuwa ga hotunananki harya ji sha'awarki?

-Shin kin shirya wa ɗaukar dukkan waɗannan zunubban?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post