An haifi wani yaro a kasar India da bindi Jama'a sun shiga harkar bautan wannan yaro



- An haifi wani yaro a kasar India da bindi
- Jama'a sun shiga harkar bautan wannan yaro
🇳🇬MA,ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE 🇳🇬
👉BY SHARHABIL USMAN PANDOSS
Wani karamin yaro dan shekara takwas mai suna Dulha Singh da aka haifa da wani abu kamar bindi a bayansa ya samu mabiya masu bauta masa.

Bindin wannan yaron ya samu asali ne daga wani tarin gashi da ya fito ma yaron a bayansa, sa’annan iyayensa sun ce yanke wannan bindi ka iya zama mummunan laifi akan wanda zai iya zuwa da mummunan sakamako.


A yanzu haka yan kauyen Amritsar, inda Dulha ke zaune da kawunsa suna tururuwa gidansa domin yi masa bauta, a yadda suke fada, sunce Dulha kwatankwancin ubangijin birai ne na addinin Hindu mai suna Hanuman.

Dayake yaro Dulha na sha’awar hawa bishiya da wasa a akai, yasa ya kara tabbatar ma yan kauyen cewa lallai shine ubangijin birai na addinin Hindu.

Wannan yasa yan kauyen suke ganinsa kamar wata rahama ne a garesu, shi yasa ma suke shafarsa domin samun tubarraki.

Wasu kuma bindin nasa suke tabawa domin samun babban tabarraki, da karama, innarsa tace “Jama’a da daman a zuwa ganinsa a kullum, sun yi amanna shine Hanuman Ji.”

 yaro Dulha baya jin komai a jikinsa, kuma baya damuwa da yadda jama’a ke son taba shi da taba bindin nasa, shi kam bai ma san dalilin da yasa jama’a ke son neman tubarraki a wajen sa ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post