Ambaton Sunan Imam Ali Dan Abu Dalib Sirrin Biyan Bukatane (AS) Kashi Na Biyu (2)!!!


🇨🇮Ma'asumah Nigerian New Update

_____________________

ABDULLAHI(1)

Dasunan Allah Mai Gigita Azzalumai Tsira Da Aminci Su tabbata Ga Annabi Da Iyalansa Tsarkaka(S).

_An ruwaito cewa, wani mutum mai suna Abdullahi Al-Haddab ya kasance mumini kuma matalauci ainun sana'ar sa itace hawa kan tsaunuka ya samo itacen wuta yakai  kasuwa ya sayar kan yan kudi kalilan.Da wandannan yan kudaden ne kuma yake biyan bukatar rayuwarsa cikin kana'antuwa da kuma hakuri, duk kuwa da cewa yana da iyali mai yawan rai bakwai, kuma dukkanin su matane.

_Ya dauki lokaci mai tsawo cikin wannan hali.Amma sai wata rana matarsa tayi alwashin cewa duk ranar juma'a zata rika fita kofar gidansu da dukudukun safiyar kowacce juma'a, har na tsawon kwanaki (40), tana addu'ar  'Naadi Ali' danufin Allah ta'ala yanuna mata wani waliyyi daga cikin waliyyansa, daza ta rokeshi alfarmar cewa ya tokar musu Allah Madaukaki ya yaye musu wannan kuncin rayuwar da suke ciki.

_To,tana cikin kokarin cika wannan alwashi nata ne, tun kafin juma'a (40)din su cika, a safiyar wata juma'a tana tsaye tana addu'arta da ta saba tana kuma yin tawassuli da Annabi Muhammad (SAW)da Iyalan Gidansa (AS), kawai sai taga wani dagon dattijo mai furfura yana tahowa daga nesa, kuma ita yadumfara kaitsaye.Koda ya iso, sai yayi mata sallama, suka kuma gaisa da juna,tana mai girmamashi.

_Daga nan sai yabar mata sako, cewa "Idan Abdullahi(Mijinta)ya dawo, kice masa duk lokacin da al'amura suka tsananta gareshi, to ya roki allah kuma yayi tawassuli da Annabi Muhammad(SAW)da iyalan gidansa(AS), sannan yawar ware addu'arsa da mawarwarin mishkiloli, wato;Naadi ali(AS).

GATA KAMAR HAKA;·👇

_Naadi Aliyyan Muzhiral-Ajaa'ib, tajiduhu Aunan laka Fil-Nawa'ib. Kulli Hammin wa Ghammin Sayanjali, Bi Wilayatika, Yaa Ali, Yaa Ali, Yaa Ali (AS).

ZAMUTSAYA ANAN INSHA ALLAH YA MUCIGABA

Masha Allah🙏

Daga Wakilin Mu Na Kano

MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com

KUKASANCE DA SHAFIN MA'ASUMAH AKODA YAUSHE DOMIN ILIMAN TUWA DA SANIN YADDA DUNIYA KE CIKI.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post