🇨🇮Ma'asumah Nigerian News Update
____________________
ABDULLAHI (2)
_Dasunan Allah Mai Mutunta Muminai Tsira Da Aminci Sutabbata Ga Annabi Da Ahali Tsarkaka
_Wannan dattijo yana gama mata wannan sako, kawai sai ta ga yabace daga gabanta kamar walkiya. Amma da mai gidanta Abdullah ya dawo gida, sai tabashi labarin abin da ya gudana. Sai mai gida yace;ayya! Ai wannan tsoho ba wani bane face khidr(S).
_To da gari ya waye, ya fita ya tafi daji, gun sana'arsa ta saran itacen sayarwa, gashi kuma lokacin hunturune dusar kankara na zubowa daga sama;ga shi kuma ya manyanta, jiki yayi nauyi. To dama a jiyan, ya tara itace da yawa a wani kogon dutse, da nufin in yaje, kawai sai ya dabo ya kawo kasuwa ya sayar, yayi cefane da kudin. Ko daya leka kogon dutse, sai yaga wayam. Itacen da ya tara bashi, sai tsibin toka kawai.
_Don wasu fatake sun sauka a gurin, kuma sunga itace nan sunyi amfani dashi donjin dumi da kuma girka abincinsu. Gashi yabar gidansa babu komai;sannan ya alkawar tawa iyalinsa cewa zai dawo da wuri, da kuma abinci mai yawa, sabo da haka da ya tarar da abin da ya tarar, sai bakin ciki da takaici suka lullube beshi, duniyar tayi mada duhu, yayin da ya tuna halin da yabar iyalinsa a ciki;kuma suna can suna jiransa ne ya dawo da abinci. Ai kawai sai ya barke da kuka da kururuwa , yana karanta du'a'in Naadi Aliyyan, harya fadi magashiyyan.
_Bayan ya farfado , ya cigaba da karanta wannan addu'ar, can, sai ya waiwaya, sai ga wani mutum a kan farin doki ya bullo masa daga gabas, fuskar mahayin dokin nan tana haske kamar wata, kamshin turaran miski daga mutumin nan kuma ya bulale guri. Koda mahayin ya iso, sai yatsaya daidai kan abdullah, kuma yayi sallama gareshi. Abdulla ya amsa. Yana gama amsa sallaman, sai mahayin dokin nan yace;"mike tsaye ya Abdullah! Hakika bukatarka ta biya. Sabo da haka sai ka debi tsakuwar dake kewayenka, kaje ka sayar da su don kayi amfani da kudin.
INSHA ALLAH ZAMU TSAYA ANAN AMMA ZAMUCI GABA
Masha Allah🙏
Daga Wakilinmu Na Kano
MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com
KUKASANCE DA SHAFIN MA'ASUMAH DOMIN ILIMAN TUWA DA SANIN YADDA DUNIYA KECIKI
Tags:
Taskar ilimi