Ambaton sunan Imam Ali Dan Abi Dalib (As), sirrin biyan bukata ne!!!

Imam Ali Wasiyyin Manzon Allah

➝MJ Matashi Ibrahim

______________________

_An ruwaito cewa; Amirul muninina Ali dan Abu Dalibi (as), wata rana, yana tafiya a wata hanya, sai ya gamu da wani mutumin Khaibara. Sai ba Khaibaren nan yayi hanzarin wuce wa gabansa. Da suka zo tsallaka wani kogi, sai ba Khaibaren ya daga mayafinsa ya taka ta kan ruwan ya haye. Sai da ba Khaibaren ya haye tukun, ya bar Amirul Muminina tsaye, sai ya waiwayo yace, daka san abin dana sani, da kaima ka hayo wannan kogi.

_Sai Amirul Muminina yace masa, kai kuma menene matsayin ka da har ruwa ya sandare maka, da ka taka ka haye?Sai ba Khaibaren yace, na roki Allah ne da Sunansa mafi girma ya Amirul Muminina. Ba Khaibaren yace, kuma sunan Wasiyin Manzon Allah(saw), A nan take Imam Ali yace masa ai nine wannan Wasiyin Manzon (saw), anan take wannan ba khaibare, wanda kafin hakan Bayahude ne ya Musulinta darajar Imam (as).

AN RUWAITO DAGA AMMAR

Yace, Wata rana naje gun Maulana Amirul muminina Ali(as), sai ya ga alamar damuwa a fuskata. Sai yacemin, meke damunka?sai nace, wanda kebin mahaifina bashine yazo don a biyashi. Sai Imam ya nuna min wani dutse da ke kusa dani, yace, dauki wannan kaje ka biya masa bashin da shi!Ammar yace wannan fa dutse ne. Sai Imam(as)yace, ka roki Allah kana mai tawassuli dani, don ya mayar maka dashi abin siyayya.

_Ammar yace, sai Na roki Allah da sunan Imam(as)din, sai dutse ya zama kudi. Sai shi kuma yace min, to dauki abin da kake bukata aciki sai nace to.

_Imam ta yaya za ayi ya sake komawa dutse?Sai yace, ya kai mai raunin yakini, roki Allah da sunana mana, ai zai koma dutsen sa. To, nidai sai na roki Allah da sunansa, kuma na debi iya abinda nake bukatata, sannan na sake rokon allah da sunansa, sai kuma ya koma dutse nan take.

_Domin kusanci da Allah wajan biyan bulata kalizimci karanta na'adi Aliyan.

Na'adi Aliyyan Muzhiral-Aja'a'ib,Tajiduhu Aunan Laka Fil-Nawa'ib. Kullu hammin wa Ghammin Sayanjali, Bi Wilayati ka,Yaa Ali, Yaa Ali, Yaa Ali.

DOMIN KARIN BAYANI SAI ADUBA

_Littafin Uyunul-Akhbaar
_Mafatihul'junan

Masha Allah🙏

       DAGA
@MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post