Abunda buhari yayima Yan shia ko fir, aunan musa baiyima bani esra, Ila ba inji shek halliru maraya

ABIN DA BUHARI YAYIMA 'YAN SHI'A KO FIR'AUNAN MUSA BEYIMA BANI ISRA'ILA BA...Inji shaikh halliru maraya
🇳🇬
MA, asuma Nigeria news update 🇳🇬
👉by sharhabil Usman pandoss

Shahararran Malamin Addinin Musuluncin nan, dake Kaduna, Sheikh Halliru Abdullahi Maraya.yayi kira ga Gwamnatin Buhari da ta gaggauta sakin Sheikh Ibrahim Zakzaky (H). In da ya kara da cewa,
"Duk kasar da ba adalci, to ba za ta zauna lafiya ba, don haka a saki Sheikh Zakzaky kawai a biya shi diyya. A kuma bashi hakuri, kamar yadda mai Shara,a a babbar kotun tarayya, justice Gabriel Kolawale ya yanke hukuncin cewa a Saki Sheikh Zakzaky da mai dakinsa, a biya shi miliyan 25, shi da mai dakinsa, a kuma gina masa gida a inda yake so cikin Arewacin Nigeria. Amma gwamnatin Nigeria taki ta bi wannan umarnin.
Sannan kuma gwamnati ta biya diyyar mutane 347 da Sakataren gwamnatin Kaduna ya ce, sun yi musu kabarin bai daya, muddun ana son dawwamammiyar zaman lafiya," inji Shehin Malamin.
Da yake magana akan abinda aka yiwa Yan,uwa musulmi a Zaria a 2015 da wasu garuruwa, ya bayyana cewa, "Abinda aka yiwa yan, shi,a a kasar nan, babu wanda aka taba yiwa irinsa a tarihin duniya. Ko fir,auna bai yi hakan ba.shi ba kowa yake kashewa ba, kuma bai yi hakan ba sai da dalili. Amma su sun kashe mata da dattijai da wanda bai san hawa ba balle sauka. Abin da suka yi ko Hitler bai yi irin sa ba, wanda ya kashe Yahudawan Jamus.....
Kadan kenan daga cikin jawabin da Sheikh Halliru Abdullahi Maraya yayi wa Mahaddata alkur,ani kuma almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) a wata  Ziyarar da suka kai masa a gidan sa dake kaduna

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post