A Ranar Lahira Makiyin Iyalan Gidan Manzon Allah (S) saiya Gwamma Ce Dama Ya Zam Mashayi Ne Ko Matsafi Anan Duniya!!!
byBin Haroun Sigau Jr-
0
Yazo cikin littafin Iqbalul A'amal Shafi na 262, Imam Jafar Bin Muhammad As-Sadiq (As) yace, "Mutum wanda yake yawan aikata aikin ɓarna ta hanyar shan giya, kamar mai bautar Tsafi ne amma maƙiyin iyalan gidan Manzon Allah (S) yafi shi."
-Wanda ya ruwaito yace, "Raina fansa gareka, me yasa yafi mai bautar Tsafi ɓarna? Imam (As) ya bashi amsa, "Ceto kan iya yiwuwa wani lokacin ga ma'abocin shan giya, amma koda dukkan abin halitta na duniya da lahira zasu taru don su ceci mai ƙiyayya da iyalan gidan Manzon Allah (S) cetonsu bazai sami karɓuwa ba."
-Allah ka ƙara manna soyayya da biyayya ga iyalan Manzon Allah (S).