ZAKZAKY: KURKUKU TARA A CIKIN SHEKARU TARA


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cewa:

"...Zuwa 1981 kuma hukuma ta fara sa ido, tana ganin abubuwan sun fara tambatsa, sun fara karfi, abin da take ganin kamar za ta maganace shi lokaci daya gashi ya fara karfi, saboda haka sai ta fara sa hannu. Lokacin kenan da aka fara kama ni a 1981 a watan Afrilu a Sokoto.

"Lokacin na je na yi wani jawabi a jami’ar Sokoto, na wuce birnin Kebbi, akwai wata Polytechnic lokacin a jihar Sokoto ta da, na je na yi lakca. To, a hanyar dawowa ne kuma suka kama ni lokacin suka ce ai shikenan na zo hannu. Sai suka bani wani irin daurin da basu ambata ba. Kawai sai da aka kai ni bakin kurkukun Inugu aka ba da ‘warrant’ wai an daure ni shekara uku.

"Sai nace ai ba haka ake daurewa ba. Har ma mun nemi lauya, lauyan ma ya je can inda nake a Inugu ya tattauna da ni, amma da ya zo daga baya yace lallai an mishi barazana, an ce masa wannan ba al’amari ne na doka ba, ba ‘legal issue’ bane, ‘security issue’ ne, in ya sa kansa zai ga abin da zai gani. Dole ya janye.

"To, lokacin kuma dai bamu samu wani gatanci ba, haka aka bar mu a kurkuku din tun daga 1981 har 1984, lokacin da aka hambare Shagari ba dadewa na fito. To, shi kuma lokacin Buhari shi kuma yana kame-kame, ba da jimawa ba wata shida tsakani aka sake kamani aka maishe ni kurkuku da sunan ‘security’. Wai saboda dalilan tsaro, wanda shima sai da aka hambare Buhari din sannan shima aka sake ni.

"Wato na fito (kamun Shagari) a watan Mayun 1984, a Decembar 1984 kuma aka maishe ni kurkukun (Buhari), kuma Augustan 1985 an hambare Buhari aka sake mu.

"To kuma bayan shekaru biyu shima Babangida ya yi nasa (kamun) a watan Maris din 1987. Lokacin ya fake da wani abin da ya faru a Kafancan, shima sai aka tattara mu haka nan dai aka kakkaimu kurkuku kamar mu ne muka yi laifin, dama ana neman sanadi. To, shima dai aka shirya wani kotu da aka yi a Abuja aka ce dai an daddauremu, daga baya aka zo aka ce an sake mu, shima bayan shekaru kusan biyu, a 1989 kenan.

"A takaice ba sai na ba da aka je rana kaza aka dawo rana kaza ba, kurkuku a wannan shekarar tamaninonin nan daga 1981 zuwa 1989, wannan tsakanin dai lallai shekaru bakwai na yi su a Kurkuku ne.

"Sannan kuma a cikin casa’inoni ma aka samu wani ‘round’ din daurin a zamanin mulkin Abacha shima. Shima shekaru biyu da kamar watanni uku. Jimla dai duka-duka na shekara 9 a Kurkuku (a baya).

"Kuma an kai ni gidajen kurkuku daban-daban wanda suka hada da Zariya da Sokoto, Kaduna, Abuja, Fatakwal da Kiri-kiri da Inugu, da ma wani waje da ake tsare mutane an ace mishi ‘interrogetion center’. Jimla dai kurkuku tara a cikin shekaru tara."

— Daga cikin Littafin HARKAR MUSULUNCI na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda Cibiyar Wallafa ke shirin Wallafa wa ba da jimawa ba InshaAllah.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post