Amma hakan bai kasance ba a cikin taimakon Allah Ta'ala. Kwatsam a kasami sauyin gwanati daga PDP zuwa APC.
Al'ummar kasa gaba daya sukayi mata kyakkyawan fata da ganin cewa za a sami sauki a raywa a kawo karshen duk wani ta'addanci a fadin Nijeriya.
Watanni 9 da hawan sabuwar gwamnatin APC sai ga wani ta'addancin da ya zarce na gwamnatin da ta shude, na PDP, domin gwamnatin APC na masu gaskiya ta zo da irin nau'in ta'addanci da aka rabu da ganin irinsa tun kusan shekaru sama da 50. Ma'an a zamanin gwamnatin farar hula ta farko a Nijeriya.
Bahaushe ya ce Ta inda aka hau tana za a sauka, Gwamnatin farar hular farko a Nijeriya ta zo da nau'in irin wannan ta'addanci da gwamnati GMB takeyi ga 'yan shi'a a Nijeriya, ita wancan gwamnatin ta NPC tayi zaluncin ne ga 'yan adawa na bangaren NEPU.
Wancan Azzalumar gwamnatin ta farar hular farko ta wanzu a cikin watanni 63 a lokacin da aka kawo karshenta da kashe jagororin wannan gwamnati a ranar 6/1/1966. Daganan wannan zalunci ya kawo karshe da azabtar da azzalumai da azzalumai, kamar yanda ahlu baiti suka labarta mana ana hukunta azzalumai da azzalumai ne.
Anyi iya yi wajen nuna ma'abota gwamnatin farar hular farko a Nijeriya da cewa su mutanen Kirki ne, anyi amfani da kafafen yada labarai wajen wanke ta'addancin wancan gwamnatin da shafa mata farin fenti.
Hakika ba zan iya mantawa da wani dan karamin littafi da na taba karantwa ba, wanda wani tsohon dan NEPU ya rubuta dangane da wahalar da yasa a hannun gwamnati NPC.
Minista a gwamnatin kama karya ta Abaca Alahji Wada Nas, ya baiyana a cikin littafin na sa na tarihin rayuwarsa, irin nau'in wahalhalun da yasha a hannun gwamnatin ta 'yan NPC, saboda tsabagen yarda da akidarsu ta NEPU suka daure akarshe kuma su sukayi nasara sakamakon dauriya da Tirjiya da kangara ga gwmnatin NPC.
Wada Nas ya ambata cewa Yana koyar a Funtua sabo da rashin biyaiyar ga gwamnatin NPC. aka dauke si aka kaishi wani kauye a matsayisa na malamin makaranta dan NEPU aka haramta ma dukkan mutanen garin yin wani hulda dashi, kai hatta daliban da yake koyarwa haramun ne yayi magana da shi in ba a cikin aji ba. An harmata masa hatta a sayar masa da abinci a garn. in yana son ya sayi a binci sai yayi tafiyar kilomita 2 kafin ya samo abin da zai ci. Amma a haka ya daure a bisa akidarasa na Kyamar zaluncin azzaluman gwamnatin NPC da akeyi wa lakabi da masu gaskiya.
Yar mahaifiyata ta taba bani wani tarihi na irin ukubar da wasu 'yan NEPU masu kyamar zalunci da meman 'yancin dan adam. Da suke a yankin kasar Bakori a yanzu suka sha a hannun jami'an gwamnatin NPC. Wata rana saboda sunki biyaiya ga gwamnatin NPC sai babban jami'in gwamnatin na Arewa ya aiko a cikin talatainin dare aka kewaye kauyen aka banka wa gidajensu masu rufin jinka wuta duk wanda ya fito a buge, a haka gwamnatin NPC ta tarwatsa wannan kauyen. amma duk da haka wannan bai sanya sun karaya ba akan ra'ayinsu na kyamar zaluncin gwamnatin NPC.
Wannan jama'ar ta 'yan NEPU na wannan kauyen suka bar kasar Katsina sukayi kaura zuwa Kasar Zazzau suka sauka a wani yanki na yankin Giwa. amma saboda bakin zaluncin gwamantin NPC sai da aka bari damina tayi sunyi noma yabanya ta samu sosai aka aiko dakarun kare zaluncin NPC suka bi wannan shukan na wadannan bayin Allahn gaba daya suka sassare ta suka sake tarwatsasu. Amma suka dake suka daure suka ki biyaiyya ga Azzaluman NPC.
Awancan lokacin na gwamnatin NPC yakasance kamar irin wannan lokacin da gwamnati APC take yakar IMN masu kyamar zaluncin azzalumai, domin neman suyi wa gwamnati biyaiya. kamar yanda 'yan NEPU suka daure suka cije akan lamarin duniya, abisa akidar da sukayi imani da ita. Ina ga ma'abota IMN da suke da akidanci na Addini kuma suna saran samun lada da sakamako gwggwaba a wurin Allah Ta'ala?
Hakika an zalunci 'yan NEPU kamar yanda ake zaluntar IMN a wannan lokacin duk da cewa abinda akeyi wa IMN a wasu fannin ya zarce na mutanen NEPU, abin da yanzu ba zai yiwu ba a ce adaina mu'amala gaba daya da IMN, wanann sai dai a mafarki.
Kamar yanda gwmanatin zalunci ta NPC da ake ga wa zaton ta adalci ce ta wanzu a cikin zaluntar mutanen NEPU a tsakanin watanni 63, amma suka daure aka sami makisa masu hambarewa sukayi wancakali da gwamnatin NPC azzaluma. Muna fata muma Allah ya tausaya mana ka aiko da azara'ilu dan yake wuyan Mujirimi na 3 a tarin Imnmuga wucewa da karshen wannan zaluncinna gwamnatin PDP da APC ga IMN, Kasanya muga karshensu gaba dayansu a cikin watanni 63 daga waki'ar na Kudus. kamar yanda labarin yake a surar Namli.
Gwanantocin baya sunyi iya yinsu na gain sun rufe bakin zaluncin da Gwamnatin NPc tayinga 'yan NEPU, amma tabbas a wannan karon tarihi bazai taba mantawa da tarihin zaluncin da akayi ga IMN ba. Domin akwai banbanci a tsakanin NEPU da IMN nesa ba kusa.
Hakika taimakon Allah tana nan kusa, in har munyi hakuri mun daure. " .....Kuyi wa masu hakuri albishir " da baiyanar Imam Mahdi(A).
Ya Allah muna jiran sake ganin su Saiyid (H) a cikin boyuwarsa daga shahararsa na tsawon adadin karamin lissafin Dawil, ka kaddara mana kaiwa lokacin da shine kake nufi na sake baiyanar a garemu, Ya Allah kabamu dauriya a cikin wannan musibar. ka gaggauta baiyanar mana da Imam Mahdi(A), domin kawo karshen zalunci gaba daya a fadin duniya.
Muhammad Sani Ra'is, Funtua
07034595991
17/2/1438 = 17/2/2016
Tags:
#FREE_ZAKZAKY