Yau Rana ce da kowa ya Jaddada Bai'ar sa..!!!


Haka ta taba faruwa a zamanin Fir'auna (L.A) da kuma Musa (A.S). Bayan taqaddamar da ta auku tsakaninsu a lokacin da Fir'auna ke nuna cewa shine Allah mai kashewa mai rayawa, Musa (A.S) kuma yace a'a, Allan da ya halicci sammai da qassai shine abin bauta na gaskiya.

An ajiye rana da lokacin da za a taru tsakanin mutanen Fir'auna dana Musa (A.S) don kowa ya jaddada bai'arsa ga wanda ya aminta da shi a matsayin shine jagoransa. Lokacin kuwa shine hantsi (wato yayin da rana ta dago), kamar dai yadda aka taru yau don jaddada bai'ah.

KARANTA WANNAN:-Yanzu Haka Sunyi Mana Kawanya, awowi Sha biyu Kenan sunata Harbi !!!


To, a waccan lokacin wasu sun jaddada bai'arsu ce ga Fir'auna, yayin da wasu suka miqawa Musa (A.S) ta su. Duk da barazanar da ake fuskanta daga Fir'auna, amma hakan bai sa mabiyan Musa (A.S) canzawa ba, wasu ma daga cikin mutanen Fir'auna suka ce sunyi imani da Ubangijin Musa da Haruna, ko da kuwa za su dawwama cikin azabar Fir'auna ne ba za su canza ba.

Kamar hakane, yau kowa ya fito ya jaddada bai'arsa ga wanda ya aminta da shi a matsayin jagora. Kuma duk wanda aka miqa masa bai'ar nan an yarda da shi ne a matsayin wanda zai fitar da mabiyan nasa daga cikin halin da suke ciki.

To, nima na sami kaina daga cikin masu wannan fitar don jaddada bai'ah, amma bai'ata ta yau na qara jaddada tane ga Sayyid Zakzaky (H) wanda na aminta dashi a matsayin shine mafita, kuma ina fatan Allah ya kaini duk inda zai kai shi.

Yanzu sai mu jira sakamako muga waye zai yi nasara a duniya da lahira.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.

08126385470-08137925034

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post