'Yar Uwa 'Yar Jami'a (1)


@Ma'asumah Nigeria News Updates
@ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

Wacece Mace ƴar Jami'a?

-Anan zamu iya cewa wata yarinya ce da take da shekaru Aƙalla 20 zuwa sama, koban faɗa ba kowa yasan Macen da takai wannan minzalin cikakkakiyar macece, wacce ta balaga. Iyayenki sun yarda dake domin sun gamsu da tarbiyyar da sukayi maki yasaka suka kawoki makarantar gaba da "Secondary" shin meya kamace ki a wannan lokaci?.

-Shine a matsayin ki na ƴar uwa mai da'awar addini, kizam cikin shigar kamala ako wanni lokaci domin waje ne data shafi mu'amala da mutanen da ba muharramanki ba, shin kinsan hukuncin zaman makaranta a Muslunci da yadda zakike tafiyar da lamuranki cikin Al'umma? Mu sani a ko wanni waje da Mace ta tsinci kanta dole ta kiyaye haƙƙoƙin addini shin kasuwanci take karatu ne koma menene, yana da kyau tasan hukuncin Allah a ciki.

-Addini ya bawa mace damar komi na rayuwa kamar yadda maza suke tafiyar da tasu, amma in muka kula zamu ga ita mu'amalarta cikin mutane abu ne mai tsauri, don haka tana da bukatar sanin hukuncin Allah a dukkan hulɗa da zata fara tsakaninta da mutane a makaranta ne ko wajen kasuwanci da sauransu.

-Kafin mu tura ƴan matanmu makarantar Jami'i yana da gayar muhimmanci mu zaunar dasu muyi musu bayani akan wanene muharrami daba muharrami ba, duk da wasunsu yawanci sunsha karatun addini yadda ya kamata sunsan komi game da Hijabi tsakanin wanda ba muharrami ba.

-Ko wacce babban makaranta zaka gan suna da tsarin saka kaya "Dress Code" ta ɓangaren maza ko mata, amma mu Allah (T) ya gama fitar mana da "Dress Code" ɗin kayan da zamuyi rayuwa dasu a addinance wanda inka danganta dana makaranta da suke saka doka akai zamu ga namu yafi cikar kamala domin duk abinda addini yazo dashi zaga shi maƙura ne.

-Amma wajibinmu ne mu ƙara tunasarsa da ƴaɓ uwan a ko wanne lokaci, bayan sun dawo hutu ne ko kuma mun kai musu ziyara ne! Sabida yawanci ƴaƴanmu a Jami'a sukan cenja daga tarbiyyar da muka ɗorasu, hakan na faruwa ne dalilin biyewa ƙungiyoyin kawaye  waɗanda kilam ma su ba Musulmai bane, ko kuma al'adunsu yana cin karon da addini.

-Wasu kuma Musulman ne amma basu damu da addini ba, irinsu suna ganin ai yanzun suna "Free World" ne domin ba mai takurasu tunda ba suna kusa da iyayensu bane ba mai tsawatar musu, amma sun manta yardar da iyayen nasu sukayi dasu yasa suka basu wannan damar ta zuwa karatu da fatan al'umma nan gaba zasu moresu.

-Da yawan Sustocinmu sukan aje maganar addini in suka shiga makarantun gaba da "Secondary" har sai sun dawo gida ne zaka gan suna damuwa da abubuwan da ya shafi addini, yakamata ƴan uwana mu dawo hankalinmu musan cewa shifa addini ba abune da ake ware masa lokaci ko wuri ba, dolenmu rayuwarmu gaba ɗaya ta ɗamfaru akan yiwa Allah (T) biyayya da gudun saɓa masa a duk inda muka tsinci kawukanmu.

-Zamu ga Jami'a waje ne na mutane da Ilimi ne ya haɗa su, hakan zai bamu damar yin da'awarmu da kambama kiran addini cikin sauƙi, domin shi mai ilimi kullum neman ƙarin sanin abinda bai sani ba yake, kinga ƴar uwata anan zaki bada naki gudunmawar kamar yadda Ummah Zeenat tayi lokacin suna Jam'a tare da Sayyid (H) wanda shi Jagoranmu ma daga nan ɗin ya faro kiransa.

-Nasan Sistoci zasu tambaya taya zasu bada nasu gudunmawa alhali kullun suna karatu da ƙoƙarin rugu-rugun "Test" da "Assignment" to, kalli wannan naganar tawa.....
Da'awa bawai yana nufin saikin tara mutane ko ƴan uwanki mata kina ce musu kaza da kaza sune abinda addini yace ayi ba.

-Dama fa bawai basu san addini bane a'a sun sani kawai dai anaso mu Masu da'awar addini mu gyara mu'amalarmu tayau da kulum ta yadda zasu ɗau ɗarasi ki zama kinfi ko wacce Mace a ajinku kamunkai da kula da rufe tsaraici ta hanyar sanya kamilallen kaya daidai da koyarwar addini duk da nasan Matan mu ƴan Jami'a basu cika son saka "Complete" ba a makaranta.

-Abu na biyu kizama nai ƙoƙaru ta tadda ko wacce a ajinku zataji tana son haɗa alaƙa dake don karuwa da abinda kike da, wannan zai baki damar ɗaukar "Attention" na mutane gaya. Domin Manzon Allah (S) baiyi nasarar kafa addini ba saida kyawawan ɗabi'u da kyautatawa mutane ta hanyar riƙon amana, taimakon marasa ƙarfi, da yalwata musu tun kafin su ɓuƙata daga gareshi bugu da kari riƙon amana.

-A ko wanni lokaci kika tsinci kanki madubinki yazam manyan bayin Allah saiki ga mutane suna ƙara tuɗaɗowa domin ɗaukar darasi daga rayuwarki da neman sanin addini daga gareki, wannan yana daga gudunmawar da Sistocinmu zasu bada don gyara zamantake war ƴan uwanmu Mata na Jami'a.

Zanci gaba in Allah ya aramin lokaci.

           ┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post