-An ruwaito cikin littafin Amali na Sheikh Al-Mufid, shafi na 49.
An ruwaito daga Musa Bin Ubaidullah daga Muhammad Bin Ka'ab Al-Qurzi ya karbo daga Awf Bin Malik yace,
-Manzon Allah (S) wata rana yace, "Na matsu in hadu da Yan uwana." sai Abubakar da Umar suka ce "Muba yan uwanka bane? Munyi imani dakai munyi hijira tare dakai.
-Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalan gidansa yace, "ba shakka, kunyi imani kuma kunyi hijra tare dani, amma duk da haka na matsu in ga yan uwana, ya kara maimaita abinda ya fada.
-Sai yace, "Ku sahabbai nane, amma yan uwana sune wadanda zasu zo bayan kun gushe. Zasui imani dani, su soni, su taimake ni, kuma su zam masu yakini akaina ba tare da sun taba ganina ba."
Taya bazan so in hadu da yan uwa na ba!
-Allah kasa muna cikin wadannan yan uwa na Manzon Allah da yake bishara damu.
┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈