Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta Saki Yan Daudu guda 30 Bayan sun yi Sallar Dare Raka’a 40

Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta kama wasu gungun yan daudu guda 30 a yayin da suke shirin aiwatar da wata mummunan badala a wani gida dake cikin birnin Kano, kamar yadda rahoton BBC Hausa ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Dakta Aliyu Musa Kibiya ne ya tabbatar da haka ga majiyarmu inda yace da fari jami’an Hisbah sun fara kama wani matashin dan daudu ne, inda a wayarsa suka jiyo wani shiri da abokansa yan daudu suke yi na yin gangami a wani gida.
“Bayan sun gama taruwa don yin wannan biki ne sai hukumar Hisbah ta dira gidan, inda ta yi nasarar kamasu duka, kuma wasu daga cikinsu sun tabbatar mana da cewa dukkaninsu yan daudu ne banda mutane uku, kuma abin haushi iyayensu ma basu san suna daudu ba.” Inji shi.
Shugaba Kibiya ya kara da cewa: “Alhamdulillahi mun zaunar dasu sun yi ta yin sallolin nafila da ma tsayuwar dare ba don komai ba sai domin wani lokaci idan kaga dan adam na aikata wani mummunan aikin, zuciya ce ta lalace.”
Daga karshe shugaban yace kowanne daga cikin yan daudun sai da ya yi salla raka’a arba’in arba’in, inda yace dama hakan na daga cikin tanadin da hukumar Hisbah ke yi ma masu laifi, saboda sallah na korar duk wani shaidani dake tattare da mutum.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post