Yadda zaka gano wajen da wayarka take, idan ta bata ko aka sace!!

Cen a baya ana amfani da Bluetooth ko kiran Number wajen gane wayar da ta bata ko aka sace, amma yanzu anyi ittifaqi wayoyi wajen Million 70 suna bata ne ba tare da layi ba ko ama cire layin.


Yanzun Android sun kawo mana mafita da baka da bukatar sai akwai layi a wayarka zaka gano inda take bayan ta fadi ko an sace.

Abinda kake bukata shine tun kafin wayarka ta bace ya zam kana da kwalinta, in kuka baka da zaka iya duba Number IMEI din ta hanyar dannna Wadannan nunbers din *#06#, numbobi ne guda sha biyar (15).

Da wadannan number zaka yi amfani wajen gane wayarka.

Abubuwan da kake bukata sune:


1- Android phone V4.4 ko abinda yai sama.

2- Find my lost phone.

3- Find my device.

4- Seekdroid.

Sunanan a Google Play bila adadin, yawancin su suna amfani da IMEI ne wajen gano waya.

Bi wadannan matakan:-

1- Yi searching do n daya daga wadannan application din na sama bayan ka Installing dinshi saika saika shiga ciki.

2- Bayan ka shiga ciki saika bawa application din damar amfani da komi na wayar da ka bufe shi dashi, kamat su yin amfani da Memory, hotuna, camera, kira Numbobi da sauransu sabida nemo wayarka da zakayi yana bukatar wadannan suyi amfani.

3- Saika dannan Continue domin ci gaba da aikin da kake son yi. Wadannan Application tracer suna da sauki saidai abu guda shine, suna zuwa da wadu 'ads' yan short Video da saika bude ka kalla kana zasu baka damar zuwa mataki na gaba, don haka kana da bukatuwar ka kalli ko wanne din din.

4- Bayan ka gama wannan zasu baka wajen saka IMEI din wayarka, saika dannan su. Idan ka gama loda su saika dannan "Track" karamin shagai zai bude da lis din sunayen wurare dauke da wajen da wayarka ke kusa dashi.

Saika je wajen don bincika wayar ka......

Insha Allah wannan shine darasin mu na yau.

Dan uwanku
Bin Haroun Sigau
08065008703.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post