Yadda Wa'azin 'Yan Shi'a ke bani Mamaki !!!


Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

@ MA'ASUMA NIGERIAN NEWS UPDATED @
Shinan kowane kuma babu wanda ya isa ya rantse cewa babu cigaba ta fuskacin kiraye-kiraye ko kuma nace wa'azi.
Abin nufi shine, yawan masu wa'azi da kuma yinsa akai-akai ya yawaita fiye da yadda ake yinsa a baya.

A bangaren Sunni, za ka ji duk lokacin da aka kafa wa'azi koma bayan wa'azin ranar juma'a a masallatai, babban abinda ke jan hankalin masu saurare shine muryar da ke tasowa daga bakin alarammomi ko kuma nace masu jan baqi ga masu wa'azin.
Wannan na daga cikin abinda mutane ke ganin shine wa'azi da aka fi so, ba wai ma'ana ko fassarar abinda ake karantawa ba.

Abinda ke daure kai ciki kuma shine, za ka iya jin ruwan ayoyi, amma kuma idan ka ji dalilin da yasa aka jawo su sai kaga kowanne da inda yasa gaba. Ma'ana, ba a kawo ayoyin a muhallinsu, sai dai don cimma wata manufa ta qashin kai.
Sai kaga an kai qarshen wa'azin amma ba shi da wata ma'ana !

Su kuma wa'azin 'yan Shi'ah in ba ka saurara bane ba za kayi saurin fahintar wa'azi ake yi ba, domin ba za ka ji ruwan ayoyi na tashi akai-akai ba.
Shi yasa wasu ke cewa labari kawai ake bayarwa !

Sai dai kuma mamakin da nake yi ciki labarin da suke bayarwa shine, ba za ka iya taba kawo aya ko hadisi wanda zai iya soke wannan labari nasu da suke bayarwa ba.
Gaskiya wannan abu na ban mamaki !
Ko menene dalilin hakan ?

Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034-08136385470

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post