"Da yawa Daya Cikin Annabawa Kashe su Akayi "!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @Shafi Domin Kai da Al'ummar ka
________________________________________
Sunnar Allah ba ta canzawa, kafin zuwan fiyayyen halitta Muhammad (S.A.W.W) an sami 'yan'uwansa Annabawa (A.S) da yawa, kuma daga cikinsu kashe su akayi.
Shima (S) ya bi sahun 'yan'uwansa, domin ba mutuwa ta al'ada yayi ba, a'a, guba aka ba shi da qarfin tsiya aka dura masa yasha ba bisa son ransa ba, wanda hakan yayi sanadiyyar Shahadarsa (S.A W.W).
A'imma (A S) ma tarihinsu bai buya ba gare mu, yawancinsu guba aka basu tayi sanadin tasu shahadar.
To, a daidai wannan lokaci sai tsinannan Allah wanda ba shi da kyakkyawan asali Buhari ya sanyawa Sayyid Zakzaky (H) guba a inda suka tsare dashi, burinsu shine yabar duniya don su sami damar yin mulkinsu ba wata barazana.
KARANTA WANNAN:- Yanzu haka sunyi mana kawanya , kusan awowi Sha biyu sunata harbi!!
Abinda suka kasa fahinta saboda qarancin imaninsu ga Allah shine, Allah shi ke karbar ran bawansa in yayi nufin haka, amma in bai nufi karbar ran nasa ba babu wani mahalukin da ya isa ya kashe shi, domin karbar rai a hannun Allah take.
Annabi Ayuba (A.S) babban misali ne, babu wata irin jinyar da baiyi ba wacce har ta kai gabobin jikinsa na gutsirewa yana faduwa qasa, tsutsotsi na cin naman jikinsa, amma da Allah yaga damar rayar dashi sai da ya zama tamkar wani abu bai taba samun lafiyar jikinsa ba.
Saboda haka wannan aiki naka BUHARI, ka sani ba za ka taba cin nasara wajen Ubangijin da ba kayi imani dashi ba.
Ko da ran Sayyid (H) ya fita daga gangar jikinsa, to, kaima ba ka isa ka dawwama a duniya ba tunda uban-uban-ubanka Fir'auna bai dawwama ba, sannan qarshenka ba zai taba yin kyau ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.