Tare da Muhammad Jiddah Nguru
08069306985
-A bisa al'ada Mu anan garin Nguru, bayan an daura aure abokan ango Sukan karbo hayar plastic chairs su samu karkashin bishiya Mai Sanyi su Zauna a wuni ana hidimar biki, abokai su hadu ayi tayin hira ana Shan Shayi, Muna kiransa (zaman angwanci)
-Jiya Naje Wurin Zaman angwancin abokina Musa SAFNA ina zaune sai ga Wani abokina Mai suna Muhammad Salis (Al-gurawi) Wanda ya Shahara a Social Media Wajen yin rubutun batanci ga 'Yan Shi'a, bayan Mun gaisa dashi Muka fara hira dashi.
-A cikin hirar tamu cikin Alfahari yake cewa 'Yan Sunni sun fi 'Yan Shi'a Yawa a fadin Duniya. Sannan Ahlul-Sunnah sun fi Shi'awa bada gudumawa ta fuskaci ilimi a da'irar addinin Musulunci.
-Sai nayi Murmushi nace Masa "Tabbas haka ne Ahlul-Sunnah Sun fi 'Yan Shi'a Yawa.
-Sai nace Masa "Yana da kyau ka gane cewa karanci da rashin Yawa ba shine Ma'auni na gane cewa Mutane suna kan bata ko halaka ba! asali ma Muslunci ya fi zargin Yawa akan karanci, amma Mafi Yawan zargin da Allah Yake yi Yana tafiya ne ga Mutane Masu yawa, kuma mafi yawan yabon da Allah ke yi a Alkur'ani yana zuwa ga Mutane 'yan kadan,
Misali: a cikin Suratul (A'araf 17) da kuma Suratul (Bakara 100) da Saratul (Imran 110,) da Saratul (An'am, 37) da (Tauba, 8).
-Wallahi Ayoyin da suke zargin yawa suna nan a cikin Alkur'ani sannan wasu ayoyi na Alkur'ani
sun yi ta yabon mutane 'yan kadan, Misali Allah Yana cewa "sau da yawa jama'a kadan sukan rinjayi jama'a masu yawa da izinin Allah "(Bakara). Haka kuma a cikin Suratul (Anfal, 34) da suratul (Saba'i, 13).
-Sai na kara ce Masa Algurawi "Idan Yawa Shine Ma'aunin gane Mutane suna kan Shiriya, to sai na ce tabbas Ahlus Sunnah sun fi 'Yan Shi'a Yawa a Duniya, to amma kuma kiristoci da Yahudawa sun ninka Ahlul Sunnah yawa a duniya.
-Idan Kuma muka koma fagen bada gudumawa ga addini sai nace 'yan shi'a sun fi kowa ta wannan bangaren.
-'Yan shi'a ne a kan gaba Wajen ba da gudumawa a da'irar Musulunci a fagen Ilimi, tunda shi ilimi shine jigon komai.
-Misali limamin Masu tafsirin Alkur'ani a cikin tabi'un, Sa'id bin Musayyib shima Dan Shi'a ne.
-Wanda ya fara tattara ilimin Ulumul Kur'an, Muhammad Bin Umarul wakidy, shima Dan shi'a ne.
-Wanda ya kirkiro ilimin Hadisi Ulumul Hadith ko Musdala'il Hadith, Abu Raafi'i shima Dan Shi'ane.
-Wanda ya fara yin Rubutu akan Fikihu ko Furu'a a duniya wato Aliyu Bin Abiy Raafi'i, Dan shi'a ne.
-Sannan Abdullahi Bin Abiy Raafi'i Wanda shine Mutum na farko da ya fara rubuta Tareekh, shima Dan shi'a ne.
-Wanda ya fara Rubutu akan seerah a duniya, Abban Bin Usman Al'Ahmar, Dan shi'a ne.
-Wanda Ya assasa Ilmul kalam, Hashim Bin Muhammad Bin Hanafiyya, Dan shi'a ne.
-Wanda a ka san Ilimin Nahwu a wurinsa Abu Aswadud-Du'aly, Dan shi'a ne.
-Limamin luggar Larabraci na Duniya, Amr Bin Uthman Dan Shi'a ne.
-Sai nace masa Algurawi "Ina ganin badan 'Yan Shi'a ba! da Addinin Musulunci ya zama tarihi.
-Nan take Al-gurawi Ya saki baki Yana kallona, sai nace Masa ku rinka yin karatu don neman Yardar Allah badan kuyi jayayya ko Musu da Mutane ba.
-Saboda haka ina kira ga 'Yan uwa Ma'abota wulaya Mu kara godewa Allah ta'ala da ya yi mana Wannan ni'imar ta riko da Wasiyar Manzon Allah (S), Sannan kuma riko da Wasiyar shine yake tabbatar da cewa Muna kan tafarki Madaidaici.
-Malamin Sunnah Imam Shafi'i ya ce: " iyalan gidan Annabi sune wanda Allah ya farlanta Mana son su a cikin Alkur'ani Mai girma, kuma ya ishe su girman Matsayi cewa duk wanda bai yi Salati gare su a cikin Sallah ba! hakika ba shi da Sallah.
-Imam Shafi'i Yace "Idan nunawa zuriyar Annabi Soyayya shine rafidanci to Mutane da Aljannu ku Shaida da ga Yau ni barafidene.
-Saboda haka 'Yan uwa Musulmi ku zo mu shiga jirgin tsira, Saboda Allah na nufin ya kawar da kazanta kawai daga gare ku, ya ku mutanen Babban Gida kuma ya tsarkake ku tsarkakewa su (MA'SUMAI NE) basa sa6awa umarnin Allah ta'ala ko kadan wallahi bin su ne kawai shiriya kin su ne bata da halaka.
-