Watarana Imam Aliy (As) yaje Kasuwa Don Sayan Tufafi , Sai Ya Hadu da Wani Kyakyawan...


-Yazo a wata ƙissa wata rana Imam Ali (As) yaje kasuwa don sayan tufafi, sai ya haɗu da wani kyakkyawan mutum.

-Imam (As) ya tambayeshi, "Kana da riguna biyu da basu wuce Dirhami biyar ba?" sai matashin ya miƙe tsaye yace Ya Amirul Mu'mineen! ina da abinda kake buƙata.
-Da Imam Ali (As) ya fahimci mutumin ya ganeshi, sai ya bar shagon ya tafi izuwa wani da yake mallakar Bayi.

-Imam Ali (As) yace, "Kana da riguna biyu wanda basu wuce Dirhami biyar ba?" Mutumin yace, "Ina da riga guda da take ta Dirhami uku, da ɗaya kuma wadda take ta Dirhami biyu".

-Imam ya kawo riguna biyun yace wa Qanbar wanda yake riƙe masa kaya, "Ka ɗauki wadda take ta Dirhami uku sabida kanka" Qanbar yace, "Kai ya kamata ka ɗauki mai tsadar, sabida kana hawa Munbari kayi Huɗuba, kayan zasuyi maka kyau sosai".

-Imam Ali (As) ya bashi amsa, "Yakai Qanbar, har yanzu kai yaro ne, kuma matasa suna ƙaunar abubuwa da yawa" zanji kunya a gaban Allah in danganta kaina a matsayin wanda ya fika.

-Sabida naji Manzon Allah tsira da aminci su ƙara tabbata gareshi yace, "Ku tufatar da masu ɗaukar kaya kamar yadda kuke wa kanku, ku ciyar dasu da irin abinda kuke ci."
Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad.....

Don ƙarin bayani a duba Rawdat Al-Waizin, Mj 1, Shafi na 107.

┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post