*WANI ABU DA YAKAMATA DUNIYA TAJI*



Game da 'Yan'uwa 60 da Alkalin High court Apo Abuja ya tura su Gidan Yari Jiya Laraba.
          Kusan mutum 20 daga cikin su a Asibitin Gwagwalada aka kwashe su, wasu ma har an sa musu ruwa Amma Haka Jami'an tsaron Buhari suka je Asibitin nan sukayi ruwan wuta suka kwashe 'Yan'uwan nan. Wasu sun warke ba tare da kaisu asibiti ba.

Masu Manyan Raunuka kuwa sune
    1. Muhammad Muhammad Gabarin (Baballe):- Akwai harsasai wuri biyu a kafar shi baya iya tafiya sai ya rike wani.
    2. Musa Muhammad Taraba:- Yanada harbi a cinyar shi baya iya tafiya dakan shi.
    3. Imrana Ayyub Faska:- Sun fasa mishi kafa da harsasai musamman Idon sawu, ko mikewa tsaya baya iya wa don haka daukar sa akeyi.
    4. Fatima Ibrahim Dasuki:- Daliba a College of Health Technology Tsafe Tana aji biyu. Akwai harbi jikin ta kamar ya warke amma yana damun ta da zafi.
    5. Ummu Kulsum Isma'il Kaduna:- Tana Pharmacy 400 level a ABU Zaria. Akwai harbi a hannun ta kusa da Kafada ko yau da badeji nannade da hannun.
    6. Muhammad Khamis Azare:- Yaro ne dan shekara goma sha daya (11) sun karya cinyar shi da harsashi har yau basu dora shi ba kwaurin shi yayi siriri ko motsa kafar baya iya wa tana damun shi da zafi, In dai ba mara Imani kamar Mahukuntan Najeria ba kana kallon yaron zaka fashe da kuka.
Tsawon wata biyar mutanen nan basu sake su ba, basu kaisu asibitin da za'ayi musu aiki ba sai dai kawai a wanke asa bandeji, Basu kaisu Kotu ba tun 22/07/2019 Sai 27/11/2019.
Jiya Kuma da aka dawo don yanke Hukuncin bada beli Kotu ta hana beli ta tura su Gidan Yari sai watan biyu na sabuwar shekara 05/02/2020
Wannan wace irin kasa ce?
Wace irin Gwamnati ce wannan fajira azzaluma?
Allah don tsarkin zuciyar Annabi Muhammadu ka rusa Gwamnatin Buhari.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post