@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE @ Shafi Domin Kai Da Al'ummar ka
Ba na siyasa ballantana na nuna bangaranci tsakanin kudu-da-arewa, ko kuma musulmi da kirista , amma dai yanayin wannan qasa tamu Nigeria yadda ta jagwalgwala da nau'in mutane azzalumai , marar sa yin gaskiya, handama da kwadayi daga malamai , to, a gaskiyar magana ta adalci Buhari ne ya fi dacewa da cancantar mulkar wannan qasa.
Hujjata kan wannan magana ita ce dogaro da hadisin Manzon Allah (S.A.W.W )da ke cewa;
‘’ WANI ZAMANI ZAI ZOWA AL'UMMATA , YAYIN DA SHUGABANNINSU ZA SU KASANCE AZZALUMAI, MALUMANSU SU KASANCE MASU HANDAMA DA RASHIN GODIYA , MASU IBADARSU KUMA BISA RIYA, 'YAN KASUWARSU SU KASANCE MASU CIN RIBA DA 'BOYE AIBUN (kayansu )CIKIN SAYE DA SAYARAWA, MATANSU KUMA SU SHAGALTU DA GYALGYALIN DUNIYA .
TO, A WANNAN YANAYI SAI A 'DORA MUSU MAFI SHARRIN CIKINSU A KANSU , ZABABBUN CIKINSU KUMA SUYI TA ADDU'AH (don neman samun sauqi da mafita )AMMA BA ZA A AMSA MUSU (cikin gaggawa ) BA ‘’.
(BIHARUL-ANWAR, J:23, SH:22)
A maganar adalci shine, babu mai kokwanto cewa a daidai wannan lokaci qasarmu Nigeria na cike da irin wadannan mutane, saboda haka akwai buqatar a samar musu shugaba daidai da su, shine Allah yaga babu wanda ya dace da su kamar Buhari , kuma ku ma shaida ne domin ganin lalacewar tata (Nigerian )kowa daga cikinku ke cewa,
‘’ NIGERIA SAI BUHARI ‘’ !
Nima kuma da nayi nazari sai na gano hakan har ma na gaskata nake fadin
NIGERIA SAI BUHARI !!!
Daga wakilan mu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda .
~ 20th December , 2019.