Tsakani da Allah har yanzu ba’a fara aikin Wutar Mambila ba – Ministan Lantarki

Tsakani da Allah har yanzu ba’a fara aikin Wutar Mambila ba - Ministan Lantarki
Ministan Lantarkin Najeriya



Sabon Ministan Lantarkin Najeriya, Sale Mamman, ya bayyana cewa maganar fara aikin Lantarki ta Mambilla, tatsuniya ce.
DABO FM ta tattaro cewa Ministan ya bayyana haka ne yayin wata ganawarshi da sashin Hausa na BBC.
Ministan ya kara da cewa; Rashin cimma matsaya tsakanin gwamnatin jihar Taraba da gwamnatin tarayya ne ya hana fara gudanar da aikin Lantarkin na Mambilla.
Sai dai ya bayyana cewa bayan kama aiki da yayi, kasancewarshi dan jihar kuma abokin gwamna, hakan ya bada damar gwamnatin jihar ta amince, an cimma matsaya domin fara gudanar da aikin.
Da yake amsa tambayar “Dama da ake ta maganar an fara aikin Lantarki, maganar tatsuniya ce kenan?”
Ministan ya shaida cewa; “Gaskiya, fisabillilahi, gaskiya guda daya ce, abin kamar da tatsuniya a ciki.”
Tin dai a shekarar 2017, gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari ta bayyana amincewa da bayar da kwangilar aikin Wutar Lantarkin Mambilla wanda zai kasancewa matattarar samun Lantarki mafi yawa a Najeriya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post