Tasirin Macce da Sunan ta a Facebook ko WhatsApp (Social media).


Ita mace ta kasance tamkar wata poster ce wacce ake amfani da ita a wajen siyasa ko kuma tallace-tallace a shaguna ko kuma kanfanoni.

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka.


Kai, ko da ace wani programme ne ake so yayi tasiri, to sai an hada dasu kafin kafin kaga armashin sa.

Wannan tasiri nasu yasa suka zama (stars) a yanar Gizo, walau ta hanyar sunayensu ko kuma hotunan su.

Yanzu idan aka ga sunan mace a yanar Gizo (FB) sai kaga anyi caaa wajen neman hada alaqa da ita, ko da kuwa namiji ne yayi amfani da sunanta da hotonta.


DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

Tabbas, cikin masu amfani da dandalin sada zumunta a (FB), za ka iya samun 30% daga cikin masu amfani da sunan mata, maza ne.

Yanzu mace za tayi rubutu (post), ko da kuwa SANNUNKU ta rubuta, matuqar tana da abokai (friends) masu yawa sai kaga anyi (likes da comments) fiye da 100 cikin qanqanin lokaci. Amma in namiji ne yayi (post) mai ma'ana, kafin kaga (likes da comments) masu yawa sai ka share kwanaki, wani lokaci kuma komai dadewarsa ba za ka gani ba.

A gaskiyar magana, in da ace wasu matan ana ganinsu ne a zahiri, to, wataqila saboda muninsu ko qazantarsu ba zai bari wani yayi mutsi ta dalilin ganin saqon su ba.
Zan iya bada misali da wani rubutuna da nayi a shekarar da ta wuce, ina jin dai ko a watan (march ko june) ne 2018 me taken
" ZANYI ADDU'AH, KU AMSA DA AMEEN KO ILAHEEY "
To, a gaskiya har rubutun ya gama yayinsa banyi tsammanin an sami (comments) 70 ba.

Abin mamaki! Kwazam sai jiya naci karo da rubutun a (profile) na wata sister, amma naga (likes) sun kai 300, (comments) kuwa wajen 3659.

Daga na qara tabbatar da cewa, ashe mata na da matuqar tasiri wajen isar da saqo.
Har nake cewa lalle da sisters namu masu mu'amala da (social media) za suyi amfani da iliminsu da fasaharsu, lalle da zasu taka rawa ta gani wajen isar da da'awar Sayyid Zakzaky (H).

Amma abin takaici, sai ya kasance suna amfani da wannan damar tasu ce kawai wajen bude (Babuka) na soyayya.
Ado Isah Guda

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post