@ MA'ASUMIYAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A lokuta dabam-dabam Manzon Allah (S.A.W.W) yakan fito da Sayyidah Ma'asuma Fatima (S.A) gaban Sahabbansa don ya nuna musu matsayin ta gare su.
Cikin riwayar da aka karbo daga Mujaheed yake cewa; Manzon Allah (S.A.W.W) ya fito yana riqe
da hannun Fatimah (S.A) sai yace;
" Wanda ya santa ya santa, wanda kuma bai santa ba, to, ita ce zuciyar da ke cikin qirjina, wanda ya cutar da ita haqiqa ya cutar dani, wanda kuma ya cutar da ni haqiqa ya cutar da Allah."
(Kashful-Ghumma)
To, a irin wannan gabatarwar da yake yi ne ga Sahabbansa dangane da matsayin Fatimah, wata rana yake ce musu;
" Mala'iku sun kasance suna ta yiwa Allah tasbihi da tsarkake shi, sai Allah mai girma da daukaka yace:
" NA RANTSE DA GIRMANA DA 'DAUKAKATA, ZAN SANYA LADAN WANNAN TASBIHI NAKU (da kuke yi) HAR RANAR ALQIYA GA MASOYAN WANNAN MACE (Fatima), DA BABANTA DA MIJINTA DA KUMA 'YA'YANTA ."
Salman yace; sai Abbas (R.A) ya tashi ya fita , sai ya hadu da Imam Ali (A.S) ya rungume shi a qirjinsa ya sumbaci goshinsa yace;
" Tabbas! Ku Ahlul-Bait tsatson Mustapha (S.A.W.W) babu wanda ya kai ku girman daraja a wajen Allah."
(Irshadul-Qulub)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034