Tarihin Imam Hasan Al-Askari (As)

Daga takaitaccen tarihin Imam Hasan Askari.

Cikakken sunan sa shine Hasan, sunan mahaifin sa Ali. Shine Imami na sha daya (11) cikin imaman shiriya, ana kiran sa da Abu Muhammd da kuma Ibn Al-Ridha.

Sabida Sammara, nan ne wajen daya rayu, gari ne na sojoji. Anfi sanin sa da Suna Al-Askari (Askar kalma ce ta soja a yaren larabci).

Imam Al-Askari ya auri Narjis Khatun, ya kare kusan ilahirin rayuwarsa ne a firizin (Prison). A ruwayar Shi'a yazo cewa; an shayar dashi guba ne bisa umurni Al-Mu'tamid, kalifan Abbasiyawa yana dan shekara ashirin da takwas (28).

An bisne shi a Sammara, shine wanda har yanzu muke jiran bayyana dan sa Muhammad Al-Mahdi, Al-Muntazir. Wanda zai cika duniya da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya.

An haifi Imam a shekarar 231 alif hijira, a garin Madina. Haihuwarsa ta faru ne lokacin da Mutawakkil yayi wa Mahifin sa canjin waje daga Madina zuwa Sammara, anyi sabani akan wannan cewa; an haife shi a Madina ne ko Sammara.

Mazhabar Shi'a sun kawo an haife shi ne a Madina 8 ga watan Rabiu Sani, yayi wafati a Sammara kasar Iraqi 8 ga watan Rabiul auwal shekara ta 260.

Yayi Imamanci na tsawon shekaru shida, an tafi dashi Sammara shida iyalin sa, a shekarar 230,231 zuwa 232Ah. An aje shi matsayin kamamme. Ya kare rayuwar sa cikan karanta Qurani da littafan shari'a.

Yazo a ruwaya Imam yayi karatun yarurruka, sanannen abu ne Imam yakan yi magana da Indiyawa da yaren su na India, Mutanen Turkiyya kuma da yaren Turkish kana yakan yi magana da yaren Persia.

Koba komi, Wannan kebantaccen ilimi ne da Allah madaukakin sarki, ke kimtsa wa Imami yasan dukkan yaruka al'ummar sa.

Yazo a ruwaya cewa; Iman Askari tun yana karami, yasan ilimummuka. Wata rana wani mutum yazo wuce shi yana kuka, mutumin yace wa Imam zai saya masa abin wasa yake wasa dashi sai Imam yace; "Ba'a halicce mu don wasa ba."

Mutumin yayi mamakin maganar Imam. Sai mutumin yace to, sabida me aka halicce mu? Imam ya amsa da cewa; "Sabida sanin ilimi da bauta wa Allah." Mutum ya kara tambaya a ina kasan wannan? Imam Askari (As) yace, daga fadin Allah da yake cewa; "Kuna tunanin mun halicce ku ne kawai bisa kaddara".

Mutumin bai gushe ba yana tambayar Imam to, me ya faru dakai kake kuka, yakai karamin yaro? Imam yace "Kayi nesa dani don naga mamana tana hada wuta da manyan itatuwa, wutar bata kama ba saida aka hada su da kanana. Kuma ina tsoron in kasance daga kananan mahadan wutar jahannama."

Mahaifiyar Imam Askari, baiwa ce ba kamar uwayen sauran imamai ba. Ana kiranta Ummu walad, wasu suna kiran ta da 'Susan, Gazala, Haribta'. Imam yana da wasu yan uwa, a cikin su akwai Jafar, wanda ake kira da Jafar Al-Zaki ko Jafarus Sani, dayan kuma Shine Husain wanda dashi da Imam Askari ana kiran su da As-Sibtayn.

Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhammad...

Allah ya yalwata kirjin mu da ninka soyayyar mu kan wannan gida mai albarka...

Almajirin ku
Bin Haroun Sigau
08065008703.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post