A wannan rana ta tunawa da haihuwar daya daga ciki annabawa madaukaka, zan dan bamu takaitaccen tahirin haihuwar Annabi Isah (As), in kunga kuskure daga gareni ne, ina rokon Allah ya yafe min.
Bismillahir Rahmanir Rahim..
Allah yana cewa, "lokacin da mala'ika Jibril, yace, Yake Maryam! Hakika Allah yazo miki da kyakkawan labari da kalmar sa wani da sunan sa Massih Isah dan Maryam, cancantacce anan duniya da kuma lahira, ga mutanen da suke masu kusanci gareshi" Aali Imran, Sura ta 3, aya ta 46.
DANNA DOWNLORD KA DAUKO WAKAR DA AKAYIWA ANNABI ISAH (AS) ACIKIN WAYARKA YANZU GATANAN AKASA
DOWNLORD
Annabi Isa (As) ana kiransa da 'Kalma' sabila da an haillicce shi ne da 'Kun fa ya kun' ba tare da uba ba. Kuma Allah ya saka shi mai kiran jama'a zuwa garesa. ana kuma kiransa da 'Massih' domin Allah ya bashi wasu abubuwa da ba kowa ke dasu ba, kamar: Tayar da matacce, warkar da makafi, kutare da yardarsa (T)."Kuma yakan iya magana da mutum tun yana dan jariri, da yayin tsufa. Sannan zai kasance daga mafi kyawun mutane" Aal Imran sura ta 3, aya ta 46).
"Tace (Sayyada Maryam) taya zan haifi da, alhali ba wani namiji daya taba, tabani?. Sai Mala'ika yace, "Duk haka, Allah yakan yi halitta yadda yaso, in yaso saidai yace kasance, kuma ya kasance. Zai karantar dashi littafai, zaboorah da injeela kuma ya maishe shi Manzo ga yayan Isma'el, kuma yazo daga Allah tare da alami."
A wata ayar kuma Allah (T) ya qara cewa, "Sai muka ambaci Maryam a cikin littafi lokacin data fito daga gidansu zuwa wani wuri a gabashi"
Ali Ibn Ibharim ya ruwaito wata rana kafin ranar da Maryam zata haifi annabi Isah, "Mala'ika Jibrel ya ziyarci Maryam ya hura mata iska ta wajen wuyan ta wanda yakai hai cikin mahaifar ta, wanda hakan shine dalilin samuwar cikin Annabi Isah (As) a daren ranar, washe gari da safe kuma ta haife shi."
Da samuwar cikinsa zuwa haihuwar sa awa tara kawai yayi kacal, wanda yayi daidai da samuwar cikin sauran mata su suna haihuwa a watanni tara, shi kuma an haifeshi a awa tara.
Imam baqir (As) ya ruwaito cewa, "Lokacin da Jibril yazo wajen Sayyada Maryam ya busa mata iska a wuyan ta tare da riqe zaninta, hakan yayi silar samuwar cikin Annabi Isah kamar yadda jariri ke zama a mahaifar uwansa dan wata tara. Sai ta fita daga wajen yin wanka da kayan jariri kamar mace da ta kammala hada watannin ta na haihuwa tana tsammanin haihuwa ko yaushe.
Lokacin da Antinta ta ganta abin ya bata mamaki, tana jin kunya da tunanin Sayyada maryam tabar gidan Zakariyya da matarsa kamar yadda yazo cikin AlQurani mai girma: "Don haka ta sami cikin sa; ta fita dashi zuwa waje." Suratul Maryam, sura mai lamba 19, aya ta 22.
An ruwaito kuma cikin hadisin Imam As-Sadiq (As) yace, "Yazo a tarihi an haifi yaro a wata shida bai rayu ba, amma Annabi Isah da Imam Husayn (As) su sun rayu"
Allah yace a cikin Alqurani, "Zugin haifar ciki ya saka Sayyada Maryam ta koma kasar bishiyar dabino. Tace, abinda nake ji, ji nake kamar kafin in haife zan mutu, kuma babban abu ne da bazai mantu ba."
Ta buqaci ta mutu, sabida tasan mutane bazasu fahimce ta ba... Imam Sadiq (As) yace, "Duk wani mutumin kirki, wayaye bazai iya fadan wani aibu daga gareta ba."
Ali Bin Ibrahm yace, "Sabida radadin haihuwa sayyada Maryam ta fito don ta sami mafaka a wani wuri, gashi ranar, ranar kasuwa ne. Ga kasuwar ta cika da masu saye da sayarwa, ta biyo ta wajen masu yin dirka (Saqa).
Ta tambaye su inane wajen tsohuwar bishiyar dabino? Sai masu saka din suka fara tsegumi suna zundenta. Don haka sai ta bar wajen tana mai addu'a kansu da masu hali irin nasu.
Daga nan tana kara gaba taci karo da gugun wasu yan kasuwa, ta sake tambaya game da irin tambayar da tayi wa wadancen. Su suka bata cikakken kwatancen wajen da bishiyar take, tayi musu godiya tare da nema masu albarkar Allah cikin sana'ar su da karin samun masu saye.
Tana Isa wajen bishiyar ta haifo Annabi Isah (As), koda ta haifo shi sai alamun tambaya suka ziyarci zuciyar ta, tana cewa; "Na gwammace dama na mutu, yanzun me zan cewa anti na da isra'ilawa"?
Sai jaririn yayi mata magana yana cewa, "Kada kiyi bakin ciki, hakika Allah madaukakin sarki , ya sanya qoramu su kwaranya ta qarqashinki." Kamar yadda Mala'ika yace mata, "Kada kiyi bakin ciki, hakika Allahn ki ya sanya qoramu su kwaranya a karkashinki, ko ya sanya Isah da kyakkyawar nasaba."
Imam baqir (as) ya ruwaito cewa, "Lokacin kafin haihuwar Isah, qoramu duk sun kafe na tsawon shekaru, amma da haihuwarsa suka dawo da ruwa kamar ma basu kafe ba."
Allah yace, "(Maryam) girgiza bishiyar dake kusa dake, zata zobo da yayan dabino gareki. Suratul Maryam, sura mai lamba 19, aya ta 24.
Wannan kadan ne daga cikin tarihin haihuwar Annabi Isah (As) ga masu bukatar cikakken sai su duba littafan tarihin annabawa.
Ina taya daukacin al'umma Musulmai da Christian murnar ranar haihuwar Isha dan Maryam (As.
Wasallahu ala Muhammad wa ali Muhammad....
@Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ
Tags:
Munasabobi