@Ma'asumah Nigeria News Update
@Shafi Domin Kai da Al'ummar ka
-Meke ruɗarka a wannan duniyar da har kake mantawa da tanadin da akai maka a lahira madawwamiya?
-Wanni kyale-kyale kake gani da har kake burin dauwama a cikinta duniya mai ƙarewa?
-Shin dama kasan bazaka iya jure jarabawowin Allah ba, ka bari ya kawoka wannan duniya?
-Meya saka bazaka ɗau hanyar Allah ba don samun masauki mai kyau gobe lahira?
-Menene ribar daka girba a wannan duniyar, domin fiskantar ubangijinka a ranar tsaiwa?
-Shin koka manta Allah yayi alkawarin cika wuta da aljanu da mutane ne, don haka kana cikinsu ko baka ciki?
-Kenen Ashe ka shirya a kona ka yasa bazakai biyayya wa Allah ba, ka kucewa saɓa masa?
-Me yasa ka ɓata, kuma ka bari ake ƙoƙarin son ɓatar da bayin Alllah, alhali nauyi ne daya rataya a wuyanka ka kirawo su zuwa hanya madaidaiciya?
-Da zamu gane da mun maida wannan duniya gidan aiki, maimakon maidata da mukai gidan jin daɗi da holewa.
-Haƙiƙa babu wani gidan jin daɗi illah gidan Aljanna, a lahira. Shine gidan daya tara dukkan kayan morewa mara yankewa.
Allah ka azurta mu da samun Aljannarka maɗaukakiya.
┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈