Tambaya:- Ko Kun San Waye Wannan Bawon Allah Din ???


Su Azzalumai sun sanshi sun San Manufar Da'awarsa! Kuma tabbas sun hango Hatsarin da ke ciki idan suka kyale wannan Da'awar!

Amma wuri ya kure masu shiyasa suke wannan haukan.

Kai kuwa shine Gatanka, Garkuwanka, kuma da Bazarshi kake Rawa.

Amman kilan kai baka sani ba, kana ganin kamar ana maganar Akida ne! Tafiyar ta wuce tunaninka baka sani ba ne.

Amma su masu Fada dashi sun sanshi sun san Manufarsa, kuma tabbas shine Fatan wannan Al'umma.

Idan kana ganin ba haka bane, kada kayi Musharaka da masu Fada Dashi, zura Ido ka gani! Domin fada dashi bafa zai haifar da Da mai ido ba!

Akwai wani Sirri da yake Tattare da Al'amarinsa kuma wannan Sirrin ne Makomar Wannan Al'umma.

Ta yiwu kace kai dai baka yadda ba ko? To ka tsaya a haka
Kada kace Zakayi Fada ko Taimakon masu son Murkushe shi, idan ba haka ba kaima za'a nemeka a rasa! Teku ne ya balle saboda haka yi sauri ka nemi Madafa!

Mutane nata Kiraye Kiraye, cewa lallai fa Al'amarin nan akwai Fushin Allah a ciki.
Tabbas Wannan haka yake fushi kam Allah yayi da Nassin Alkur'ani Mai Girma
cewa "Duk wanda ya taba Bawansa kuma Masoyinsa Lalle Fushinsa zai sauka a Kansa" Allah (T) ya Haskaka zukatan Al'umma su gane Nufin Wannan Bawan Allah!

Fatana shine Al'umma su gane wanene Wannan Bawan Allah da ake magana a Kansa. Wannan ba kowa bane sai:
Jagoranmu kuma Maulanmu, Shugabanmu SHEIKH ALLAMAH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post